Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Nijar, an Yi Hasashen Halin da Za a Shiga a Afrika

Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Nijar, an Yi Hasashen Halin da Za a Shiga a Afrika

  • Kasar Amurka ta sanar da cewa ta fara janye dakarunta da suka kafa sansani a kasar Nijar biyo bayan bukatar da kasar ta yi a baya
  • A cikin shekaru sama da goma kasar Nijar ta kasance wajen da Amurka ke kafa sansanin Soji domin shirin yaki da ta'addanci a Afrika
  • Kasar Nijar ta bukaci sojin Amurka su tashi daga kasar ne biyo bayan juyin mulki da sojojin kasar suka yiwa Muhammad Bazoum

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Kasar Niger - Biyo bayan bukatar da kasar Nijar ta yi, Amurka ta fara janye sojojinta da suka kafa sansani a kasar.

Nijar ta nuna kin amincewa da cigaba da zaman sojin Amurka a yankin ne tun bayan juyin mulki da sojoji suka yi a bara.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Joe Biden
Amurka ta fara janye sojojinta daga Nijar. Hoto: Joe Biden
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta fitar da hasashe kan yadda lamarin tsaro zai cigaba da kasancewa a yankin bayan fara tafiyar sojojin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin Amurka sun fice daga Nijar

Kasar Nijar ta kasance cikin wuraren da Amurka ta kashe $110m wajen gina sansanin soji domin yaki da musu ta'addanci a Afrika.

Sai dai Amurka ta fara janye sojojin ta a ranar 7 ga watan Yuni biyo bayan bukatar hakan da kasar Nijar ta yi wanda a yanzu saura sojin Amurka 6000 a kasar.

Amurka ta yi magana kan janye sojoji

Kasar Amurka ta ce janye sojojin na cikin abubuwan da suka tattauna kuma suka fahimci juna da sojojin kasar Nijar.

Ta kara da cewa dama sun tattauna kan yadda za su kammala janye sojojinsu daga Nijar zuwa ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa, rahoton Voice of America.

Kara karanta wannan

Aiki da cikawa: Ana tsaka da bikin babbar sallah, sojoji sun kashe dan bindigan da ya addabi Kaduna

Ya tsaro zai kasance a yankin?

Biyo bayan fara ficewar sojojin Amurka a Nijar, an fara bayyana yadda lamarin tsaro zai kasance a yankin yammacin Afrika.

Duk da ana ganin Amurka za ta iya daukan sabon mataki na jigbe sojinta a wata ƙasa, masu hasashe sun ce za a zuba ido a ga yadda jami'an tsaron yankin za su iya yakar yan ta'adda su kaɗai.

Sojoji sun yi magana kan Bazoum

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin sojojin juyin mulkin Nijar sun bayyana cewa hamɓararren shugaban kasa, Mohamed Bazoum ba zai dawo kan mulki ba.

Janar Abdulsalami Abubakar, ɗaya daga cikin jagororin wakilan ECOWAS shi ne ya bayyana haka bayan ya gana da Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel