Tsananin Zafi: Matakan da Saudiyya Ta Dauka Domin Rage Mutuwar Mahajjata
- Tsananin zafi yana cikin abubuwan da suke tasiri sosai wajen jawo yawaitar mutuwar mahajjata a kasar Saudiyya
- Biyo bayan haka, kasar Saudiyya ta dauki shekaru masu yawa tana tanadi da shirin yadda za ta magance lamarin cikin sauki
- Bayan daukan mataki na tsawon shekaru, binciken masana ya nuna cewa an samu raguwar mutuwar mahajjata a ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Yawaitar zafi a kasar Saudiyya yana zama barazana ga rayuwar mahajjata da suka fito daga ƙasashen da ba a zafi sosai.
Biyo bayan haka, kasar Saudiyya ta dauki matakan saukaka lamarin domin kubutar da rayuwar mahajjata.
Bincike da asibitin sarki Faisal ya yi ya nuna cewa bayan shafe shekaru 40 ana daukan mataki, an samu nasarar dakile matsalolin zafi a kasar, rahoton Arab News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zafi: Matakan da Saudiyya ta dauka
1. Samar da fankoki domin rage zafi
Saboda tsananin zafi da ake fama dashi a ƙasar, an samar da fankoki da za su rika sanyaya yanayi a cikin gari.
Fankokin suna sanyaya yanayin kasar ta inda mahajjata za su samu aminci ko da suna tafiya a fili ne, rahoton Saudi Gazette.
2. Raba lemar hannu da ruwan sha
A wani bangaren kuma, kasar Saudiyya ta dauki matakin samar da lema da mahajjata za su rika yawo da ita.
Bayan haka, an samar da ruwan gora da mutane za su rika sha da zarar zafi ya musu yawa domin sanyaya jiki.
3. Jiragen kasa masu na'urar AC
A yayin tafiye-tafiye daga Makka zuwa Madina ko wasu wurare, kasar ta samar da jiragen kasan zamani.
Jiragen suna dauke da na'urar sanyaya muhalli (AC) domin rage zafin rana da kuma jin jigila cikin sauki.
Sauran matakan da aka dauka domin rage mutuwar mahajjata sun hada da samar da inuwa da za a rika hutawa, ɗaukan matakan rage cinkoso, kara ingancin asibitoci da suaransu.
Mahajjacin Najeriya ya rasu a Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya yiwa wani Alhaji da ya fito daga jihar Kebbi rasuwa a birnin Makkah yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Hukumar jin dadin Alhazan jihar wacce ta tabbatar da rasuwar Alhajin a cikin wata sanarwa ta ce ya fito ne daga Gulma cikin ƙaramar hukumar Argungu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng