Mafi Karancin Albashi: Kasashen Afrika 10 da Suka Fi Kowa Biyan Ma'aikata Albashi Mai Tsoka
Abuja - A Najeriya, gwamnati ta yi alkawarin biyan fiye da N60,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Alkawarin gwamnatin ya biyo bayan tsunduma yajin aiki da kungiyar NLC ta yi na kwanaki biyu kafin ta dakata.
Albashin karamin ma'aikaci a Najeriya
A yanzu haka ma'aikata a Najeriya suna daukar mafi karancin albashin N30,000 ne kacal wanda ba komai ba ne duba da tsadar rayuwa da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kasashen Afrika akwai ma'aikata da ke daukar makudan kudi na mafi karancin albashi, The Nation ta tattaro.
Legit Hausa ta binciko kasashe 10 da suka fi biyan mafi karancin albashi ga ma'aikata.
1. Seychelles
Seychelles ita ce ƙasa da ke biyan mafi karancin albashi mai yawa da ya kai $465.54 ko kuma N695,175 a kudin Najeriya a yau.
2. Libya
Kasar Libya da ke Arewacin Afrika ta na ba ma'aikata $321 ko kuma N489,895 a kudin Najeriya.
3. Morocco
Kasar Morocco ita ma da ke Arewacin Afirka tana biyan $314 ko kuma N469,430 a matsayin mafi karancin albashi.
4. Gabon
Kasa ta hudu ita ce Gaban da ke ba ma'aikata $270 ko kuma N403,650 a kuɗin Najeriya.
5. Equatorial Guinea
Equatorial Guinea ita ce ƙasa ta biyar da ke ba ma'aikata $211 ko kuma N315,445 mafi karancin albashi.
6. Algeria
Kasar Algeria a Arewacin Afirka tana ba ma'aikata mafi karancin albashi $140 ko kuma N209,300.
7. Cape Verde
Wannan kasa tana ba ma'aikatanta mafi karancin albashi $139 ko kuma kudin Najeriya N207,805.
8. Kenya
Kenya ita ce ƙasa ta takwas da mafi karancin albashi $130 ko kuma N194,350 ga ma'aikata.
9. Mozambique
Mozambique ita ce ta kusa da na karshe da ke ba ma'aikata mafi karancin albashi $113 ko kuma N168,935.
10. Lesotho
Sai kasa ta karshe wato Lesotho da ke ba ma'aikata $109 ko kuma N162,995 a kudin Najeriya.
NLC ta janye yajin aiki na kwanaki
Kun ji cewa Kungiyar kwadago ta NLC ta janye yajin aiki da ta shiga a ranar Litinin 3 ga watan Yuni kan batun karin albashi.
Kungiyar ma'aikatan ta tsunduma yajin aiki ne domin neman karin albashi ga ma'aikata yayin da ake cikin wani hali a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng