Ma’aikatan Birtaniya Sun Sakawa Marasa Lafiya Kanjamau a Gurbataccen Jini

Ma’aikatan Birtaniya Sun Sakawa Marasa Lafiya Kanjamau a Gurbataccen Jini

  • Bincike ya gano yadda aka yi amfani da gurbataccen jini ga marasa lafiya wajen yada cututtuka ga mutane a kasar Birtaniya
  • Tsohon Alkali Mista Brian Langstaff ne ya gudanar da bincike domin gano badakalar da ta cinye rayuka tsawon shekaru
  • Ana sa ran Firaministan kasar, Rishi Sunaki zai ba wadanda abin ya shafa hakuri tare da magana a kan yadda za a biya su diyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

United Kingdom - Ma'aikatan lafiya a Birtaniya sun jefa dubban al'umma cikin rashin lafiya sakamakon saka musu gurbataccen jini.

Gurbatten jini
Mutane sama da 3,000 sun mutu sakamakon saka musu burbataccen jini a Birtaniya. Hoto: Emma Haris
Asali: Facebook

An ruwaito cewa mutane da dama ne suka mutu sanadiyyar saka masu gurbataccen jini da ma'aikatan lafiya suka yi a kasar.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

Rahoton VOA ya nuna cewa an dauki shekaru ana saka wa mutane jinin kafin a gano lamarin cikin makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1970 - 1960: Mutanen Birtaniya da suka mutu

Daga shekarar 1970 zuwa 1990 mutane akalla 3,000 ne suka mutu sanadiyyar saka musu gurbataccen jini, rahoton BBC.

Masu sharhi suna ganin wannan badakala ita ce mafi muni a harkar kiwon lafiya a tarihin kasar Birtaniya.

Cututtukan da badakalar ta haifar a Birtaniya

Binciken da aka fitar ya nuna cewa wadanda aka saka wa jinin sun fi kamuwa da cutar kanjamau da ciwon hanta.

An bayyana cewa hakan ya faru ne daga yadda hukumomi suka rika karbar taimakon jini daga mutane daban-daban cikin har da yan fursuna.

Yadda aka gano badakalar a Birtaniya

Wani tsohon alkali mai suna Brian Langstaff ne ya yi bincike kuma ya fallasa irin ta'asar da ma'aikatan lafiyar suka aikata.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Mista Brian Langstaff ya zargi ma'aikatan lafiya da gwamnatin Birtaniya kan sakaci da lafiyar mutane.

Ana sa ran firaministan Birtaniya zai ba mutane hakuri tare da biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.

Birtaniya ta yi biris da Yarima Harry

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an gwamnatin Birtaniya sun bayyana dalilansu kan nuna halin ko in kula ga ziyarar da Yarima Harry ya kawo tarayyar Najeriya.

Hukumomin Birtaniyan sun magantu ne bayan yawaitar cece-ku-ce kan rashin jin motsin su a zahiri ko yanar gizo kan zuwan yariman Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng