Ebrahim Raisi: An Sanar da Kwanakin Zaman Makoki Saboda Rasuwar Shugaban kasar Iran

Ebrahim Raisi: An Sanar da Kwanakin Zaman Makoki Saboda Rasuwar Shugaban kasar Iran

  • Iran ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu
  • Ana kallon Ebrahim Raisi a matsayin wanda zai gaji jagoran juyin juya hali na ƙasar Ayatullah Ali Khamenei a Iran
  • Shugabannin duniya a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, sun yi alhinin rasuwar Ebrahim Raisi yayin da abokansa ke yaba masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tehran, Iran - Jagoran juyin-juya halin musulunci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya ayyana kwanaki biyar a matsayin na zaman makoki bayan rasuwar Shugaba Ebrahim Raisi.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, an bayar da sanarwar ne a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya tsoma baki kan rigimar Ministan Tinubu da gwamnan PDP

Za a yi zaman makoki a Iran
Za a yi zaman makokin kwanaki biyar saboda rasuwar Ebrahim Raisi a Iran Hoto: Atta Kenare
Asali: Getty Images

Kamfanin yaɗa labarai na Islamic Republic News Agency (IRNA) ya kawo rahoton sanarwar zaman makokin da Ayatullah Ali Khamenei ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ina sanar da kwanaki biyar na zaman makoki tare da mika ta'aziyyata ga al'ummar ƙasar Iran."

Raisi: Shugabannin duniya sun yi jimami

Firaministan India, Narendra Modi, ya ce ya yi matuƙar baƙin ciki da kaɗuwa sakamakon rasuwar Ebrahim Raisi.

Narendra Modi ya rubuta a kan manhajar X ranar Litinin, 20 ga watan Mayu cewa:

"Koyaushe za a tuna da gudummawar da ya bayar wajen ƙarfafa alakar da ke tsakanin India da Iran. Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalansa da al'ummar Iran. India tana goyon bayan Iran a wannan lokaci na baƙin ciki."

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya jajantawa al'ummar Iran.

Kara karanta wannan

Ebrahim Raisi: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba kan shugaban ƙasar Iran da ya rasu

Shugaban ƙasar ya rubuta a shafinsa na manhajar X cewa:

"Muna matukar baƙin ciki da rasuwar shugaban ƙasar Iran Ayatullah Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen ƙasar Hossein Amir-Abdollahian da kuma jami'ai. Muna miƙa ta'aziyyarmu ga Ayatullah Ali Khamenei da al'ummar Iran."

Jirgin Ebrahim Raisi ya yi hatsari

A wani labarin kuma kun ji cewa wani jirgi mai saukar ungulu wanda yake ɗauke da shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi ya gamu da hatsari.

Kafar labaran ƙasar ta ce, lamarin ya auku ne a lokacin da Shugaba Raisi ke kan hanyarsa ta dawowa yankin lardin Azabaijan ta Gabashin Iran.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng