Yakin Isra’ila Kan Hamas: Sojin Isra’ila Sun Yiwa Falasdinawa 5 Kisan Gilla a Kogin Jordan

Yakin Isra’ila Kan Hamas: Sojin Isra’ila Sun Yiwa Falasdinawa 5 Kisan Gilla a Kogin Jordan

  • A wani harin da sojojin Isra’ila suka kai kan jama’a, sun hallaka mutane biyar da aka bayyana su da cewa ‘yan Falasdinu ne
  • Isra’ila na ci gaba da yiwa mazauna yankin Falasdinawa kisan kiyashi tun bayan da fada ta sake barkewa tsakaninsu da Hamas a shekarar 2023
  • Kasashe da dama na ci gaba da yanke alaka da Isra’ila duba da yadda take yiwa yara da mata kisan gilla a Gaza da sauran yankuna

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Tulkarm, Jordan - Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa biyar a wani samame da suka kai cikin dare a wani kauye kusa da birnin Tulkarm a yankin yammacin gabar kogin Jordan, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinu da sojojin Isra'ila suka sanar a jiya Asabar.

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Lauya ya ja hankalin gwamnati kan hana dalibai masu hijabi rubuta UTME

Ma'aikatar lafiyar ta ce ta gano hudu daga cikin biyar da suka mutu a harin da aka kai a Deir Al-Ghusun.

Sojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa a Jordan
Yadda sojin Isra'ila suka kashe Falasdinawa a Jordan | Hoto: AFP
Asali: AFP

Sojojin Isra'ila sun dauki wasu gawarwakin kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinawa Wafa da kuma wakilin Reuters a wurin da lamarin ya faru suka shaida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An raunata dan sandan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce wani jami'in 'yan sanda na musamman ya samu rauni a harin, wanda yanzu haka yake kwance a asibiti.

Isra’ila ta ce dakarunta sun yi ramuwar gayya ta hanyar amfani da harsasai da kuma makamai masu linzami, Arab News ta tattaro.

Harin da aka kai a ranar Asabar shi ne na baya bayan nan a jerin gwabzawar da ake tsakanin Isra’ila da Hamas a yammacin gabar kogin Jordan da sojojin Isra'ila suka mamaye.

Kara karanta wannan

Kungiya ta maka gwamnoni 36 da minista Wike a kotu kan cin bashin N5.9tn da $4.6bn

Yadda yakin ya sake tashe a 2023

Idan baku manta ba, a watan Oktoban 2023 ne tsattsamar gabar Isra’ila ta Falasdinu ta kara kamari, inda ‘yan Hamas suka farmaki ‘yan Isra’ila.

Ya zuwa yanzu, sojojin Isra’ila sun kashe fararen hula da dama da sunan daukar fansar harin da Hamas ta kai kan Isra’ilawa.

Duniya dai na ci gaba da yiwa Isra’ila tofin Allah tsine bisa yadda take cin zarafin danadam da kananan yara da mata a ci gaba da harin da take kaiwa a Gaza.

Isra'ila za ta haramta Aljazeera a kasarta

A wani labarin, kun ji yadda firayinministan Isra'ila ya bayyana aniyarsa ta haramtawa gidan talabijin na Aljazeera aiki a kasarsa.

Ya zargi gidan talabijin din da goyon bayan Hamas tare da kara ruruta wutar rigima a tsakanin abokan gaban biyu.

Aljazeera dai na daga tashoshin talabijin da ke tattaro rahotannin cin kashin da Isra'ila ke yiwa Falasdinawa a Gabashin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.