Watanni 6 Ana Fafatawa: Muhimman Lokuta 10 a Yaƙin Isra’ila da Hamas

Watanni 6 Ana Fafatawa: Muhimman Lokuta 10 a Yaƙin Isra’ila da Hamas

A ranar 7 ga watan Oktoba, mayakan Falasɗinawa, Hamas, suka kaddamar da hari kudancin Isra'ila wanda ya yi silar mutuwar fararen hula 1,170 a cewar rahoton AFP.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wannan shi ne hari mafi muni a tarihin Isra'ila, wanda Firayin Minista Benjamin Netanyahu ya mayar da martani.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sun kaddamar da wani mummunan harin soja a yankin Gaza wanda ke karkashin Hamas, akalla mutane 33,000 ne suka mutu a harin. An ce mafi yawansu mata da kananan yara ne.

An shafe watanni 6 ana fafata yaki tsakanin Hamas da Isra'ila
Harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba ya sauya tarihin Gaza. Hoto: AFP
Asali: AFP

AFP ta yi nazari kan yadda yakin wata shida ya mayar da yankin Gaza kufai, kuma ya mayar da arewacin kasar ta koma makabartar dubunnan mutane, a cewar rahoton UN.

Kara karanta wannan

Jerin manyan mata 10 mafi arziki a duniya da adadin kudin da suka mallaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

(1) 7 ga Oktoba: Harin Hamas na farko

Da asubahin ranar 7 ga watan Oktoba, bayan kammala hutun bikin Sukkot na Majusawa, daruruwan mayakan Hamas suka kaddamar da hari kan Isra'ila ta ruwa, kasa da sama.

Aljazeera ta rahoto cewa mayakan sun kashe fararen hula a titi, sun bi wasu har cikin gidajensu, da babban dakin rawa na kasar da kuma farmakar sansanin soji.

Sun kama akalla mutane 250 a matsayin bayin yaki inda suka kai su Gaza, wasu daga cikinsu sun mutu a yanzu.

Isra'ila ta sha alwashin tarwatsa Hamas, kan kace kwabo, su ka fara sakin ruwan bama-bamai a kan Gaza.

(2) 13 ga Oktoba: Harin ramuwwar gayya

A ranar 13 ga watan Oktoba, Isra'ila ta yi kira ga fararen hula da ke zama a Gaza da su koma Kudancin kasar cikin awa 24, inda suka ayyana Arewacin kasar a matsayin 'filin yaki'.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Annabi Muhammad ke yawaita yi a kwanaki 10 na karshen Ramadan

Reuters ta rahoto dubunnan Falasɗinawa sun yi hijira zuwa Kudancin Zirin Gaza, yayin da aka mayar da Arewacin Gaza ta koma tamkar turbaya.

(3) 27 ga Oktoba: Tankoki sun shiga Gaza

A ranar 27 ga watan Oktoba, tankokin yakin Isra'ila suka fara kaddamar da mummunan harin kasa a cikin Gaza.

Mayakan suka ci gaba da sharewa kansu hanya a yunkurinsu na kutsawa birnin Gaza.

(4) 15 ga Nuwamba: An kai hari asibiti

A ranar 15 ga watan Nuwamba, dakarun Isra'ila suka kaddamar da wani harin dare kan asibitin Al-Shifa, asibiti mafi girma a Gaza, inda tuni dama magunguna suka kare, mutane suka fara mutuwa.

A cewar rahoton The Guardian, wannan harin ya jawo hankalin duniya, tare da Allah wadai daga hukumomi da kasashe daban daban.

Isra'ila ta yi ikirarin cewa Hamas na aiwatar da wani atisayen soji a karkashin ƙasar asibitin, zargin da Hamas ta ƙaryata.

A watan Maris, Isra'ila ta sake farmakar asibitin, ta kwashe makonni biyu tana kai hari, lamarin da ya yi silar mutuwar daruruwan mutane tare da lalata asibitin baki daya.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

(5) 24 ga Nuwamba: An tsagaita wuta a Gaza

A ranar 24 ga watan Nuwamba, aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon mako guda tsakanin Isra'ila da Hamas, a tattaunawar da Qatar ta shiga tsakani.

Kungiyar Hamas ta saki wasu Isra’ilawa 80 da ta yi garkuwa da su cikin kwanaki bakwai a musaya da Falasdinawa 240 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.

Isra'ila ta ba da dama a kai taimakon jin kai cikin Gaza yayin da aka tsagaita wuta, sai dai kowa na dar-dar kan zuwa kai daukin.

Lokacin da yakin ya sake barkewa, Isra'ila ta fadada hare-harenta zuwa kudancin Gaza.

(6) 12 ga Janairu: An kai hari kan 'yan Houthi

A ranar 12 ga watan Janairu, Amurka da Birtaniyya suka kaddamar da hare-hare ta sama kan wuraren da 'yan tawayen Yemen ke mulki.

Wannan na zuwa bayan hare-haren da 'yan tawayen Houthis da ke samun goyon bayan Iran suka shafe makwanni suna kai wa a kan tekun Bahar Maliya domin nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza.

Kara karanta wannan

Kisan 'Yan Sanda a Delta: An kame mutum da ake zargi da yiwa jami'ai kisan gilla

Hare-haren na Amurka da Birtaniyya ya kara haifar da fargabar barkewar wani yakin a yankin.

(7) 26 ga Janairu: An hana 'kisan kare dangi'

A wani hukunci na wucin gadi da aka yanke a ranar 26 ga watan Janairu a shari'ar da Afirka ta Kudu ta shigar, kotun kasa da kasa ta gano "a fili" cewa hare-haren Isra'ila na iya zama "harin kisan kare dangi".

Babbar kotun ta duniya ta umurci Isra'ila da ta yi "duk mai yiwuwa" don kaucewa kai harin kisan kare dangi a Gaza amma ta gaza ba da umarnin dakatar da yakin.

(8) 29 ga Fabrairu: An mutu a Turmutsitsi

A ranar 29 ga Fabrairu, sojojin Isra'ila suka bude wuta kan mazauna arewacin Gaza da suka tare wasu ayarin motocin dakon kayan abinci.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce mutane 115 ne aka bindige har lahira tare da jikkata daruruwa a wani abin da ta kira "kisan kiyashi.

Kara karanta wannan

Rikicin Jihar Plateau: Fulani na zargin sojojin Najeriya da yi masu bakin aika-aikata

Rundunar sojin Isra'ila ta ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su, mutane ne suka tattake su ko kuma manyan motocin suka bi ta kansu.".

Amurka, Jordan da sauran kasashe suka fara jigilar abinci zuwa Gaza. A ranar 15 ga Maris, babban jirgi da yayi jigilar abinci a karon farko ta hanyar ruwa ya isa Gaza.

(9) 25 ga Maris: Amurka ta bijirewa MDD

A ranar 25 ga Maris, Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a karon farko ya zartar da wani kuduri na neman tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza bayan da Amurka, wacce ta ki amincewa da daftarin da aka yi a baya, ta kauracewa taron.

Isra'ila ta mayar da martani da kakkausar murya kan kauracewar da Amurka ta yi, tare da shan alwashin ci gaba da kai hare-hare ta kasa a Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.5 ke samun mafaka.

(10) 2 ga Afrilu: An kashe ma'aikatan agaji

Kara karanta wannan

Malabu: EFCC ta gaza gabatar da hujjoji, kotu ta wanke Adoke daga zargin rashawa

A ranar 2 ga Afrilu, aka kashe ma'aikatan agaji bakwai na kungiyar agaji ta World Central Kitchen a wani harin da Isra'ila ta kai.

An ce a lokacin da aka kai harin, ma'aikatan na barin wani kantin sayar da kayayyaki a tsakiyar Gaza bayan sauka kayan abinci na jin kai.

Wadanda suka mutun sun hada da 'yan kasar Ostireliya, Birtaniya, Falasdinu, Poland da kuma Amurka-Kanada.

Kisan nasu ya jawo Allah wadai a duniya. Shugaban Amurka Joe Biden ya ce "Isra'ila ba ta yi abin da ya dace ba domin kare ma'aikatan da ke ba da agaji" a Gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.