Sarki Charles III Ya Yi Bankwana da Duniya? Gaskiya Ta Bayyana
- A ranar Litinin yanar gizo ta cika da zato da tsammanin samun 'babbar sanarwa' daga gidan sarautar Birtaniya
- Rahotanni sun nuna cewa wasu kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya
- Sai dai, kwatsam a ranar Talata, mai martaban ya bayyana wanda hakan ya kori jita-jitar cewa ya koma ga mahaliccinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Londan, UK - Akwai jita-jitar da aka yi ta yaɗa wa ranar Litinin, 18 ga watan Maris 2024, cewa Sarkin Birtaniya, Charles III, ya mutu.
Sai dai, bayyanar da sarkin ya yi a bainar jama'a a ranar Talata, 19 ga watan Maris 2024, za ta kwantar da hankula sakamakon firgicin da aka shiga kan batun mutuwarsa.
Charles: Sarki yana nan da rai
Kamar yadda jaridar The News ta ruwaito a ranar Talata, 19 ga watan Maris, an ga Sarki Charles yana isa Clarence House a Westminster yayin da yake ci gaba da jinyar cutar daji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayyanar Sarkin dai ta kawo ƙarshen jita-jitar da aka yi ta yaɗa wa cewa numfashinsa ya ƙare a duniya.
Bayan ya kwashi lokaci kaɗan a Clarence House, an nuno shi yana ɗagawa mutane hannu, kafin daga bisani ya wuce birnin Landan.
Sarki Charles ya ci gaba da aikinsa
A yammacin ranar Talata, masarautar ta rubuta a shafin Twitter cewa Sarkin ya gana da tsoffin sojojin da suka fafata a yaƙin Koriya a fadar Buckingham don bikin cika shekaru 70 da sanya hannu kan yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen yaƙin.
Wani ɓangare na rubutun na cewa:
"A safiyar yau Talata 19 ga watan Maris, Sarki ya gana da tsofaffin sojojin da suka fafata a yaƙin Koriya a fadar Buckingham domin bikin cika shekara 70 da rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen rikicin.
An kwantar da Sarki Charles a asibiti
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar Buckingham ta sanar da cewa an kwantar da Sarki Charles III a asibiti domin yi masa tiyata.
Sarkin wanda aka kwantar a wani asibitin kuɗi a birnin Landan, za a yi masa tiyatar mafitsara ne bayan ciwonsa ya ƙara tsananta.
Asali: Legit.ng