Halin Kunci: An Barke da Murna Bayan Ukraine Ta Turo Wa Najeriya Hatsi Tan Dubu 25, an Samu Bayanai

Halin Kunci: An Barke da Murna Bayan Ukraine Ta Turo Wa Najeriya Hatsi Tan Dubu 25, an Samu Bayanai

  • An barke da murna a Najeriya bayan samun tallafin tan dubu 25 daga kasar Ukraine don rage matsalar yunwa
  • Kasar Ukraine ta ba da tallafin ne don taimakawa kasar yayin da take cikin matsalar abinci musamman Arewa maso Gabas
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya da kuma tsadar kayayyaki musamman bangaren abinci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta sanar da ba da hatsi tan dubu 25 daga gwamnatin kasar Ukraine.

Kasar Ukraine ta ba da tallafin ne don taimakawa kasar yayin da take cikin matsalar abinci musamman Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Jerin ministocin Tinubu 12 da suka fi kowa kokari bayan binciken ayyukansu

Ukraine ta turo hatsi tan dubu 25 ga Najeriya don rage radadin matsalar abinci
Kasar ta aike da hatsin ne don dakile matsalar tsadar abinci a kasar. Hoto: Volodymyr Zelenskyy, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Menene dalilin turo tallafin Najeriya?

Ta ce ta ba da tallafin abincin ne don agajin gaggawa ga mutane akalla miliyan 1.3 da ke fama da matsalar abinci a yankin, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy shi ya ba da wannan tallafin na alkama don rage radadin tsadar abincin a kasar.

An samu damar kawo abincin da taimakon Burtaniya da Canada da Faransa da Norway wurinta hanyar jigilar hatsin zuwa Najeriya.

Sauran kasashen da suka dauki nauyin jigilar sun hada da Sweden da Korea da Finland da Denmark don rage matsalar yunwa, Daily Trust ta tattaro.

Martanin daraktan WFT a Najeriya

Wakilin hukumar WFT a Najeriya, David Stevenson ya ce :

”Muna mika godiya ga gwamnatin Ukraine da sauran wadanda suka taimaka wurin tabbatar da tallafin hatsin.
“Wannan hadaka ta taka rawar gani wurin rage radadin yunwa a wuraren da ke fama da matsala da rsadar abinci.”

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a cikin awa daya, Sheikh Daurawa

Matsalar hare-hare a yankin Arewa maso Gabas ya tilasta miliyoyin mutane rasa matsugunansu da gonakinsu inda ya kawo matsala a samar kayan gona.

Tinubu zai biya matasa alawus

Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya yi alkawarin biyan matasa alawus don rage musu radadin da suke ciki a kasar.

Shugaban ta bakin Ministan kudade, Wale Edun ya ce matakin ya zama dole musamman ga matasa da babu aikin yi.

Wannan na zuwa ne yayin da mutanen kasar ke cikin wani irin mawuyacin hali na matsin tattakin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.