Tashin Hankali Yayin da Sojin Sama Ya Cinna Wa Kansa Wuta, An Fadi Dalili

Tashin Hankali Yayin da Sojin Sama Ya Cinna Wa Kansa Wuta, An Fadi Dalili

  • Wani jami'in sojan saman Amurka ya nuna adawarsa kan kisan ƙare dangin da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa a zirin Gaza
  • Sojan mai suna Bushnell ya cinna wa kansa a gaban ofishin jakandancin ƙasar Isra'ila da ke birnin Washington D.C
  • Hukumomi sun tabbatar da cewa sojan mai shekaru 25 a duniya ya rasu bayan raunukan da ya samu sakamakon wutar da ya cinna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Washinton D.C., Amurka - Wani jami'in rundunar sojin saman Amurka da ya ƙona kansa a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, ya rasu

Jami'in sojin saman ya cinna wa kansa wuta ne a gaban ofishin jakadancin ƙasar Isra'ila da ke birnin Washington D.C.

Sojan saman Amurka ya rasu
An yi amfani da hoton ne kawai don misali, fuskokin da ke ciki ba su da alaka da labarin. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Marigayin ya cinna wa kansa wuta a lokacin da yake cewa "Ƴancin Falasdinu".

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da kwamishinan NPC, ya shiga muhimmin taro da jiga-jigai a Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar NBC News ta lura cewa wani jami'in sojin saman Amurka ya tabbatar mata da labarin mutuwar jami'in sojin samam

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito, mutumin mai suna Aaron Bushnell ya garzaya zuwa ofishin jakadancin Isra'ila da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu.

Meyasa sojan ya ɗauki matakin salwantar da ransa?

Jami'in ya riƙa ɗaukar bidiyonsa yana watsawa kai tsaye a kam dandalin watsa bidiyo na Twitch.

Bushnell, mai shekaru 25, ya bayyana cewa "ba zai ƙara yarda ya zama yana da hannu a wajen kisan kare dangi ba".

Jami’an tsaro sun yi imanin cewa marigayi sojan sama ya fara watsa bidiyon ne kai tsaye, inda ya ajiye wayarsa sannan ya sanya wa kansa fetur tare da kunna wuta.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sake kashe bakaken shugabannin ‘yan bindiga da yaransu

Isra'ila Ta Halaka Mataimakin Shugaban Dakarun Hamas

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani hari da Isra’ila ta kai kan mazauna birnin Beirut na ƙasar Lebanon, ta yi ikrarin cewa, hari ne kan daya daga cikin shugabannin ƙungiyar Hamas.

Mark Regev, mai magana da yawun ƙasar Isra’ila ya ce, mataimakin shugaban Hamas, Saleh Al-Arouri ya mutu a wani harin da jirgin Isra’ila ya kai kan shugabannin Hamas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng