Ba Kamar Najeriya Ba, Shugabar Kasa Ta Yi Murabus Kan Wani Kuskure 1 da Ta Yi, Bayanai Sun Fito

Ba Kamar Najeriya Ba, Shugabar Kasa Ta Yi Murabus Kan Wani Kuskure 1 da Ta Yi, Bayanai Sun Fito

  • Yayin ake ta cece-kuce kan wani mataki a Hungary, Shugabar kasar ta yi murabus daga kujerarta na shugabanci
  • Katalin Novak ta dauki wannan matakin a yau Asabar 10 ga watan Faburairu bayan cece-kuce kan yin afuwa ga wani mutum
  • Ana tuhumar shugabar da yin afuwa ga mutumin da ake zargi da cin zarafin karamar yarinya wanda bai yi wa 'yan kasar dadi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Shugabar kasar Hungary a Nahiyar Turai ta ajiye mukaminta na shugabancin kasar a yau Asabar 1 ga watan Faburairu, cewar Aljazeera.

Katalin Novak ta dauki wannan matakin bayan cece-kuce kan yin afuwa ga wani mutum da ake zargi da cin zarafin karamar yarinya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Shugabar kasa ta yi murabus kan yafiya ga mai laifi
Shugabar Kasar Hungary, Katalin Novak Ta Yi Murabus Daga Mukaminta. Hoto: @KatalinNovak.
Asali: Twitter

Mene dalilin murabus din Novak a Hungary?

An yi ta cece-kucen ne bayan daukar matakin yafewa mutumin da ake zargi da cin zarafin wanda bai yi wa jama'ar kasar dadi ba, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta:

"Zan yi murabus daga kujerata, na yi kuskure na kuma yi nadamar abin da na yi."
"Na nemi yafiya ga wadanda na yi musu ba dai-dai ba da kuma dukkan wandada suke ganin ban goyi bayansu ba.
"Zan ci gaba da kasancewa mai kare muradun kananan yara da kuma iyalansu a ko wane lokaci."

Kiraye-kirayen da ake yi ga Novak a Hungary

Novak ta na rike da mukamin tun a watan Maris na shekarar 2022 wanda ta kasance ta na da kusanci sosai da Fira Ministan kasar, Viktor Orban.

Wannan lamari ya jawo kace-nace a kasar wanda aka yi yafiyar tun a watan Afrilun 2023 bayan kokarin boye laifin da wani mataimakin darakta ya yi.

Kara karanta wannan

"Kada ka kalla idan kana da hawan jini": Matashi ya bada shawara gabannin wasan Najeriya na karshe

Tun bayan faruwar lamarin ne jam'iyyun adawa a kasar suka dukufa kiran Novak da ta yi murabus daga mukaminta.

Tinubu ya karbi murabus din Lalong

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yanke shawarar amincewa da murabus din Ministan Kwadago, Simon Lalong.

Minisan ya yi murabus ne bayan samun nasara a Kotun Daukaka Kara a shari'ar zaben sanata a Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.