'Yan Sanda Sun Tsare Tantabara Tsawon Wata 8 Kan Leken Asiri a Indiya

'Yan Sanda Sun Tsare Tantabara Tsawon Wata 8 Kan Leken Asiri a Indiya

  • Wata tantabara ta shiga hannun hukuma a kasar Indiya inda aka zarge ta da yi wa kasar Sin wato China leken asiri
  • An kama wannan tantabaran ne saboda an gano wasu kananan abubuwa masu kama da zobe a kafafuwanta dauke da na'ura
  • Binciken da aka gudanar daga bisani ya nuna cewa tantabarar ba leken asiri ta ke yi ba, ta shiga wani gasar tsere ne ta kauce hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Indiya - 'Yan sanda sun saki wani tantabara bayan tsare shi tsawon watanni takwas bisa zargin cewa shi dan leken asirin kasar Sin (China) ne.

'Yan sandan kasar Indiya a Mumbai sun tsare shi ne an gano shi a watan Mayu da zobe biyu a kafarsa dauke da rubutun harshen China, kuma an gano karamin na'urar a daya cikin zoben, rahoton UPI news.

Kara karanta wannan

An gano gawar 'yar jami'ar Najeriya a dakin kwananta

An kama tantabara kan zargin yi wa China leken asiri a Indiya
An tsare tantabara na watanni takwas a Indiya bisa zargin yi wa China leken asiri. Hoto: Anshuman Poyrekar/AP
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda masu bincike sun tsare shi a asibitin Bai Sakarbai Dinshaw na Dabobi kan zargin yin ayyukan leken asiri a madadin China.

An mika tantabarar ga Kungiyar Hana Cin Zalin Dabobi kuma ta sake shi ya yi tafiyarsa a ranar Talata.

Menene masu bincike suka gano kan tantabarar?

Binciken da 'yan sanda suka yi ya tabbatar da cewar tantabarar ba dan leken asirin China bane, amma ya shiga gasar tseren ruwa ne a Taiwan kuma ya kauce hanya, ya kare a Indiya.

Kungiyoyin kare hakkin dabobi PETA Indiya ta yi maraba da sakin tantabarar da ta dade tana kiraye-kirayen a saki tsuntsun.

Meet Ashar, shugaban sashin yaki da cin zalin dabobi na kungiyar, cikin wata sanarwa da ya fadawa New York Times ya ce:

"PETA India na samun kira-kirayen neman daukin gaggawa na dabobbi fiye da 1,000 duk mako, amma wannan ne karon farko da aka samu batun sakin wanda ake zargin dan leken asiri ne."

Kara karanta wannan

Yobe: Mayakan Boko Haram sun kai hari a cibiyar tattara sakamakon zabe, sun kashe mutum 2

India Ta Rushe Masallacin Juma’a Mai Shekaru 600 a New Delhi, an Lalata Kaburbura a Wurin Ibadar

A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin Indiya ta rushe masallacin Juma’a mai dimbin tarihi aNew Delhi, babban birnin kasar.

Masallacin akalla ya kai shekaru 600 a duniya wanda ya ke dauke da tarihi na musamman a kasar, cewar rahoton TRT World.

Wannan rushe masallacin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gangamin cewa a rushe masallatan don maye gurbinsu da wuraren bautar Hindu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164