Dangote Zuwa Otedola: Masu Kudin Afrika 20 da Adadin Dalolin da Suka Mallaka a 2024

Dangote Zuwa Otedola: Masu Kudin Afrika 20 da Adadin Dalolin da Suka Mallaka a 2024

  • Femi Otedola ya samu matsayi a sahun mutane 20 da suka fi kowa arziki a nahiyar Afrika
  • Baya ga shugaban kamfanin na Geregu Power, akwai ‘yan Najeriya uku da sunayensu ya fito
  • Aliko Dangote ne kan gaba kasashen Afrika, Mike Adenuga da Abdussamad Rabiu sun yi zarra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban kamfanin lantarki na Geregu Power, Femi Otedola shi ne mutum na 20 a sahun masu kudin Afrika a shekarar nan.

Mujallar Forbes ta saki jerin attajiran nahiyar Afrika inda aka ga sunayen ‘yan Najeriya hudu.

Dangote da Adenuga
Attajiran Afrika, BUA, Dangote da Adenuga Hoto: Getty Images, Forbes
Asali: Getty Images

Otedola ya shigo layin su Dangote

Arzikin masu kudin ya karu a ‘yan watannin bayan nan daga $81.5bn a shekarar 2023 zuwa $82.4bn, ma’ana sun samu karin $900m.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi maganar ficewar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC da takarar 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Najeriya kuwa Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu da Mike Adenuga suka fi kowa kudi kamar yadda The Cable ta kawo rahoto a jiya.

Arzikin Dangote ya karu da $400m zuwa $13.9bn domin ya tsare matsayinsa a jerin Forbes bayan an kifar da shi kwananakin baya.

Johann Rupert mai $10.1bn shi ne na biyu sai takwaransa na kasar Afrika ta Kudu, Nicky Oppenheimer yana matsayin na uku a nahiyar.

Na hudu kuwa shi ne Nassef Sawiris wanda ya sha gaban shugaban kamfanin Globacom, Mike Adenuga da akalla fam dala biliyan 1.8.

Har ila yau wani mutumin Afrika ta Kudun, Christoffel Wiese ya dawo cikin sahun farko.

Su wanene masu kudin Afrika a yau?

1. Aliko Dangote — $13.9b

2. Johann Rupert da danginsa — $10.1b

3. Nicky Oppenheimer & family — $9.4b

Kara karanta wannan

Zargin cin hanci: EFCC za ta binciki ‘dan siyasar da ya fi kowa dadewa a majalisa

4. Nassef Sawiris — $8.7 b

5. Mike Adenuga — $6.9b

6. Abdulsamad Rabiu — $5.9b

7. Naguib Sawiris — $3.8b

8. Mohamed Mansour — $3.2b

9. Koos Bekker — $2.7b

10. Patrice Motsepe — $2.7b

11. Issad Rebrab & family — $2.5b

12. Mohammed Dewji — $1.8 b

13. Strive Masiyiwa — $1.8b

14. Aziz Akhannouch da danginsa — $1.7 b

15. Othman Benjelloun da danginsa – $1.4b

16. Youseff Mansour — $1.3b

17. Yassen Mansour — $1.2b

18. Christoffel Wiese — $1.2 b

19. Michiel Le Roux — $1.1b

20. Femi Otedola — $1.1 b

Dangote, BUA da Adenuga ne gaba a Najeriya

Kwanaki rahoto ya zo cewa an yi sabon na biyu a jerin gawurtattun masu kudin Najeriya wanda ya zarce Alhaji Abdussamad Rabiu.

Ba a dade ba aka ji shugaban Globacom, Mike Adenuga wanda ya gwabje mai kamfanin BUA, ya rasa wannan matsayi a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng