"Ku Nema Yanzu": Gangariyar Dama Ga Malaman Najeriya Masu Son Aiki a Amurka Ta Samu

"Ku Nema Yanzu": Gangariyar Dama Ga Malaman Najeriya Masu Son Aiki a Amurka Ta Samu

  • Babban dama ya samu ga malamai yan Najeriya su shiga wani shiri na bada horaswa don zama kwararrun malamai a Amurka.
  • Shirin na makonni shida na kuma ya kunshi taron kara ilimi a jami'ar da za ta dauki nauyi shirin tare da bada gurbin aikin koyarwa a wasu makarantu a yankin.
  • Wadanda suka yi nasara za su samu damar koyarwa a aji, koyar da yan tawagarsu da koyar da abin da suka koya ga sauran malamai da dalibai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Amurka - Shirin koyarwa na 'Fulbright Teaching Execellence and Achievement Program' yana gayyatar malaman Najeriya da wasu zuwa wani shirin bayar da horasawa na sati shida a Amurka.

Yayin shirin za a gudanar da tarurukan kara ilimi a jami'ar sannan daga bisani a bada guraben koyarwa a wasu makarantu a yankin.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

Guraben aiki ga malaman Najeriya a Amurka
Dama ta samu ga malaman Najeriya su samu aiki a Amurka. Hoto: @FulbrightTeach
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cancanta

A cewar FTEAP, an bullo da shirin ne domin malaman makarantun sakandare daga kasashen da aka zaba.

Yayin shirin, wadanda suka samu damar zuwa za su samu damar koyarwa a aji, koyar da yan tawagarsu da koyar da abin da suka koya ga sauran malamai da dalibai.

Mahalarta shirin kuma za su yi samu damar yin ayyukan cigaban al'umma da al'adu a garuruwan da aka karbi bakuncinsu.

Ofishin jakadancin Amurka ta sanar da guraben ayyuka 7 domin yan Najeriya

A bangare guda, Legit.ng ta rahoto cewa Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ta sanar da wasu guraben ayyuka da dama domin yan Najeriya, tare da albashi mai tsoka.

Wannan aikin zai bai wa yan Najeriya dama yi wa Gwamnatin Kasar Amurka aiki kuma a biya su albashi a kudaden kasashen waje.

Kara karanta wannan

Daga karshe iyayen yar shekara 4 da aka aurawa dan shekara 54 sun magantu

A cewar wata sanarwa daga shafin yanar gizo na Amurka, an bude guraben ne ga yan Najeriya da ke Legas da Abuja. Hakazalika, ofishin jakadancin ta karfafawa yan Najeriya wadanda ke sha'awar aikin gwiwa su nemi aikin kafin wa'adin rufewa ya yi.

Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya Za Ta Fara Daukan Sabbin Ma’iakata

A wani rahoton, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya na neman kwarararru da masu karatun sakandire su cike bukatar neman aiki a hukumar da ta bude kofa.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa daga shafin hukumomin tsaron farar hula, gidajen gyaran hali, hukumar kashe gobara da shige da fice (CDCFIB) a intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164