Attajirin Najeriya Dangote Ya Sullubo da Aka Fito da Jerin Farko na Masu Kudin 2024

Attajirin Najeriya Dangote Ya Sullubo da Aka Fito da Jerin Farko na Masu Kudin 2024

  • Mai kudin Najeriya Aliko Dangote shi ne na biyu a jerin manyan attajiran nahiyar Afrika a shekarar nan
  • Alkaluma sun nuna Mista Johann Rupert na kasar Afrika ta Kudu ne kadai ya sha gaban fitaccen attajirin
  • A jerin masu kudin Afrika akwai Abdul Samad Rabiu da shugaban kamfanin Globacomm, Mike Adenuga

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Africa - Masu kudin Afrika sun fara shekarar nan ta 2024 kamar yadda aka san su a bara. Mujallar Forbes ta fitar da jerin attajiran duniya.

Ko a sabuwar shekarar nan da ake ciki, babu wanda ya kai Johann Rupert a Afrika.

Aliko Dangote
Johann Rupert, Nicky Oppenheimer da Aliko Dangote Hoto:Bloomberg/Contributor. Getty
Asali: Getty Images

Johann Rupert yana gaban Dangote?

Mujallar ta ce arzikin Johann Rupert ya karu zuwa $10.3bn, a lissafin da aka yi a ranar Talatar nan, Alhaji Aliko Dangote yana da $9.5bn.

Kara karanta wannan

NNPC na rikici da ‘yan kasuwa, ana zancen litar fetur ta haura N1200 a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu dukiyar Aliko Dangote ba ta karu ba a shekarar nan. Wannan ne mafi karancin kudin da attajirin ya mallaka a shekaru goma.

Forbes ta ce a duk fadin duniya, shugaban kamfanin na Dangote shi ne mutum na 230 a cikin manyan masu kudi, Rupert kuma yana 192.

Aliko Dangote ne na 1 ko na 2?

Daga $25bn a shekarar 2014, arzikin ‘dan kasuwan Najeriyan ya dawo $9.5bn. Hakan bai rasa nasaba da karya Naira da aka yi kwanan nan.

Amma a rahoton Bloomberg, har yanzu Dangote ne attajirin da ya fi kowa a Afrika.

Lissafin Bloomberg ya sha bam-bam inda aka ga sunan mai kudin a mutum na 128 a duniya, ana tunanin ya mallaki $15.1bn a 2024.

Shi kuwa Rupert shi ne na biyu da $12.4bn, alkaluman sun ce shi ne attajiri na 162 a duniya sai dangin Nicky Oppenheimer su na biye.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai yi wa ma’aikatan Kano karin kudi saboda cire tallafin man fetur

Su wanene masu kudin Afrika a 2024

1. Johann Rupert: $10.3bn

2. Aliko Dangote: $9.5bn

3. Nicky Oppenheimer & Family: $8.3bn

4. Nassef Sawris: $7.4bn

5. Abdul Samad Rabiu: $5.9bn

6. Nathan Kirsh: $5.8bn

7. Issad Rebrab and Family: $.6bn

8. Mohammed Mansour: $3.6bn

9. Naguib Sawris: $3.3bn

10. Mike Adenuga: $3.1bn

Mutuwar mutane a kasar Iran

Ana bikin tunawa da mutuwar Qasem Soleimani, sai labari ya zo cewa an kai hari a kabarinsa a Iran, har aka kashe Bayin Allah 103.

Ana yi wa marigayin kallon shahidi ganin yadda ya yaki ISIL. Soleimani ne ya jagoranci rundunar Quds kafin a kashe shi a 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng