Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Zub Da Hawaye Yayin Da Ya Roki Mata a Kan Su Kara Haihuwa, Bidiyo

Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Zub Da Hawaye Yayin Da Ya Roki Mata a Kan Su Kara Haihuwa, Bidiyo

  • Bidiyon shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, yana rokon iyaye mata a kan su haifi karin yara ya yadu
  • A bidiyon da ya yadu a yanzu, Kim ya bukaci mata da su dakatar da raguwar da aka samu wajen yawan haihuwa don taimakawa wajen karfafa karfin kasar
  • Bukatar Kim ya bambanta da shirin hana haihuwa da aka bullo da shi a shekarun 1970 da 80 don rage karuwar jama'a bayan yaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya gaza shanye hawayensa yayin da ya roki iyaye mata a kan su kara yawan haihuwar 'ya'ya domin taimakawa wajen karfafa karfin kasar.

Kamar yadda Sky News ta rahoto, Kim ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron ranar iyaye mata na duniya a Pyongyang.

Kara karanta wannan

"Sun yi zaton damfara nake yi": Mai aiki a gidan mai ta dau wanka ta bayan aiki, bidiyon ya yadu

Shugaban kasar Koriya ta arewa ya zubar da hawaye
Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Yi Kuka Yayin da Ya Roki Mata a Kan Su Kara Haihuwa, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: @dannmuts
Asali: Twitter

A cikin bidiyon da ya yadu, an gano shugaban Koriya ta Arewa mutum mai karfin zuciya yana share hawaye da farin hankici.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwararru sun yarda cewa iyalai da dama basu da sama da 'da daya a Koriya ta Arewa saboda "suna bukatar makudan kudade wajen tayar da yaransu.

"Ya ku iyaye mata, hana raguwar yawan haihuwa da kuma kula da yara da kyau duk ayyukan tsare gida ne da muke bukatar aiwatarwa yayin aiki tare da iyaye mata.
“Wadannan ayyuka sun hada da tarbiyyar ‘ya’yansu, ta yadda za su daukaka ci gaban juyin juya halinmu, kawar da dabi'un da basu dace ba, inganta zaman lafiya tsakanin iyali da hadin kan al’umma, samar da ingantacciyar hanyar rayuwa ta al’ada da kyawawan dabi’u, samar da kyawawan dabi’u da halayen taimakon juna da ciyar da juna gaba sun mamaye al’ummarmu, tare da dakile raguwar haihuwa, da kula da yara da tarbiyyar su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

"Wadannan abu ne da ya zama gama gari cikin harkokin iyalinmu, wadanda ya kamata mu yi maganinsu ta hanyar hada hannu da iyayenmu mata."

Kiran da Kim ya yi cikin zubar da hawaye ya sha banban da shirin hana daukar ciki da Koriya ta Arewa ta bullo da shi a shekarun 1970 da 80 don rage karuwar jama'a bayan yaki.

Shugaban Koriya ta Arewa ya hana dariya

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasar Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya haramta wa 'yan kasar sa nuna kowacce irin al'amari farin ciki na tsawon kwanaki 11 domin cikar shekaru 10 da rasuwar Kim Jong-Il.

Kamar yadda rahotannin The Telegraph suka bayyana, wannan alamun nuna farin cikin sun haramta a bayyana su kama daga dariya ko shan giya na tsawon kwanaki 11 domin makoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel