Kashe-Kashe a Zirin Gaza: Jerin Ƙasashen da Ke Goyon Bayan Isra'ila
- Yaƙin Isra'ila da Falasdinu na ɗaya daga cikin tashe-tashen hankula na baya bayan nan da suka addabi duniya, yayin da sojojin Isra'ila ke cigaba da luguden wuta a zirin Gaza
- Hakan ya faru ne bayan shekaru biyu da sojojin Rasha suka fara mamaye ƙasar Ukraine da ke makwabtaka da ita
- Tun lokacin da Isra'ila ta fara kashe-kashe a Gaza, sama da mutane 9000 ne aka bayar da rahoton cewa an halaka su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƙasashen duniya dai na ta fama da tashe-tashen hankula, wanda na baya-bayan nan shi ne tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.
Bayan kusan shekaru biyu da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, duniya ta sake fuskantar wani yaƙi inda Isra'ila ta kai hari kan al'ummar Gaza bayan harin da ƙungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar Asabar 7 ga watan Oktoba.
Me ya sa Isra'ila ke kai wa Falasdinawa hari
Harin na Hamas ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,400, sannan aka yi garkuwa da kusan mutum 230, cewar rahoton BBC Pidgin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hare-haren ramuwar gayya, Isra'ila ta kai hare-hare a zirin Gaza tun bayan harin, kuma adadin fararen hula da suka rasa rayukansu ya kai 9000 ya zuwa ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba, a cewar hukumomin Falasɗinu.
Sai dai, ƙasashe daban-daban na duniya sun ɗauki matakin goyon bayan Isra'ila duk da fararen hulan da take kashewa da laifukan yaƙi da ta ke aikatawa. Ƙasar Amurka na kan gaba-gaba wajen goyon bayan Isra'ila.
Amurka na goyon bayan Isra'ila
Amurka ta bayyana ƙudirinta ga al'ummar Isra'ila, inda ta ƙara da cewa goyon bayanta ga tsaron Isra'ila zai kasance mai ƙarfi.
Bayan aukuwar harin na ranar 7 ga watan Oktoba, shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya tabbatar da ƙasar Amurka a matsayin babbar ƙawar Isra'ila, ta fannin tattalin arziƙi da soja.
Tun bayan harin Hamas fadar White House ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Benjamin Natanyahu. Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyara kafin ziyarar Shugaba Biden.
Biden ya yi watsi da kiran tsagaita wuta a Gaza kuma yana matsawa majalisar dokokin ƙasarsa ta amince da ƙunshin taimakon sama da dalar Amurka biliyan 14 don kare sojojin Isra'ila.
Sauran ƙasashe da ke goyon bayan Isra'ila aya ga Amurka, sun haɗa da:
- Ƙasar Ingila
- Jamus
- Faransa
- Italiya
- Ƙasashen Gabashin Turai kamar Hungary da Jamhuriyar Czech
Majalisar Dattawa Ta Bukaci a Tsagaita Wuta
A wani labarin kuma, majalisar dattawa ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da ta kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Hamas.
Majalisar ta kuma buƙaci gwamatin tarayya da ta shiga tsakani domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe fiye da wata ɗaya.
Asali: Legit.ng