An Kama Mutane 4 Kan Laifin Satar Bandaki Na Gwal Daga Fadar Blenheim

An Kama Mutane 4 Kan Laifin Satar Bandaki Na Gwal Daga Fadar Blenheim

  • Za a gurfanar da wasu mutane hudu bisa tuhumarsu da laifin satar bandaki na zinare da aka kiyasta kudinsa ya kai fam miliyan 4.8
  • Wadanda ake zargin sun yi awon gaba da bandakin a fadar Blenheim a watan Satumbar 2019, a wani samamen dare da suka kai
  • An taba sanya ban dakin zinaren a gidan kayan tarihi na Guggenheim da ke New York, a shekarar 2016, inda mutane 100,000 suka yi layi don amfani da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ingila - An tuhumi wasu mutane hudu bisa laifin satar wani bandaki na zinari da aka kiyasta kudinsa ya kai fam miliyan 4.8, wanda ya bace daga Fadar Blenheim a wani samame na dare da wasu barayi suka kai a watan Satumban 2019, kamar yadda rahoton jaridar Guardian UK ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Janar Alkali: An samu ci gaba yayin da lauyan mai kara ya gabatar da muhimmiyar shaida

A cewar rahoton jaridar, bandakin zinaren, da ake wa lakabi da suna Amurka, wani bangare ne na baje koli na mai zane-zanen Italiya Maurizio Catelan.

Maurizio Cattelan’s America
Ana tuhumumar wasu mutane hudu da satar bandaki na zinari da kudinsa ya kai £4.8m daga fadar Blenheim Hoto: Jacopo Zotti (Guggenheim Museum 2016)/PA
Asali: Twitter

A ranar Litinin, hukumar gabatar da kara ta 'Crown', ta ce ta bayar da izinin tuhuma kan aikata laifi akan wasu mutane hudu, wadanda za su gurfana a gaban kotun majistare ta Oxford, a ranar 28 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ake yi da bandakin zinaren?

Bandakin zinaren, wanda za a iya amfani da shi a kayyadadden lokaci na minti uku don kauce wa layi, ya kasance a wajen bajen kolin na tsawon kwanaki biyu kawai, kafin wadanda ake zargin suka sace shi.

An ajiye bandakin zinaren ne a matsayin aikin fasaha a fadar Oxfordshire, mahaifar Winston Churchill, lokacin da ya bace.

Kamar yadda aka girke shi a lokacin, cire shi ya haifar da ambaliya da lalacewar kyakkyawan gidan da ya wanzu tsawon karni 18 da kuma wani sashe na wurin tarihi na Unesco a Woodstock.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa wani harsashi har lahira yayin gwada maganin bindiga a Bauchi

Gidajen tarihi da aka taba ajiye bandakin zinaren

A cewar rahoton jaridar The Punch, an taba sanya bandakin zinaren a gidan kayan tarihi na Guggenheim da ke New York, a shekarar 2016, inda mutane 100,000 suka yi layi don amfani da shi.

Daga bisani aka yi kaura da shi zuwa Blenheim, inda aka ajiye shi a cikin dakin da ke fuskantar dakin da aka haifi Churchill, a wani wasan kwaikwayo na farko da Cattelan ta Birtaniya za ta gabatar bayan fiye da shekaru 20.

Matukin jirgin sama ya mutu a bandaki yayin ja jirgin ke gudu

Legit Hausa ta ruwaito maku wani abin tashin hankali da ya faru da fasinjojin jirgin sama 271 da suka taso daga Miami zuwa Chile, inda mataukin jirginsu ya yanke jiki ya faɗi matacce a yayin da ake sheka gudu a sararin samaniya.

Matukin wanda aka bayyana sunansa da Ivan Andaur, ya fara jin alamar rashin lafiya bayan sa'o'i uku da tashin jirgin na kamfanin LATAM daga Florida zuwa Santiago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel