Sheikh Gumi Ya Bude Asusun Ba Da Gudunmawa Ga 'Yan Falasdinu
- Shahararren malamim addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya bude asusun taimakon Falasdinawa
- Gumi ya bayyana haka ne a yayin karatunsa inda ya shawarci Musulmai su ba da tasu gudunmawa
- Ya ba da asusun banki wanda za a yi amfani da shi don tura gudunmawa ga 'yan kasar Falasdinu
Jihar Kaduna - Sheikh Ahmed Gumi ya bude asusun da za a yi amfani da shi don taimakawa Falasdinawa yayin da ake ci gaba gwabza yaki.
Gumi ya bayyana cewa za su yi wannan aiki ne don taimakawa mutanen Falasdinu yayin su ke cikin wani yanayi na zalunci daga Isra’ila.
Wane shiri Gumi ke yi na taimakon Falasdinawa?
Shehin malamin ya bayyana haka ne a faifan bidiyo a jiya Juma’a yayin wani karatu inda yace ya zama dole su taimaka.
Bashin Karatu: Kamata Ya Yi Dalibai Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin, In Ji Mai Fashin Baki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shawarci sauran malamai da su hada kai don ganin sun gayyaci wakilin Falasdin da ke ofishin jakadancinsu a Abuja don ba su wannan taimako.
Ya ce:
“Ya kamata mu kawo wakilin Falasdinawa nan mu yi musu addu’a Allah ya warkar da marasa lafiyarsu da wadanda su ka jikkata da kuma wadanda su ka yi shahada."
Wane shawari Gumi ya bai wa Musulmai?
Ya kara da cewa:
“Mu ma Musulmai mu tara musu gudunmawa na taimako ko nawa ne, su na da wakili a ofishin jakadancinsu a Abuja, mu rubuta a hukumance mu na son ganinshi.
“Sannan duk masallatai su tara akai ofishin jakadancinsu, Amurka taimakon me takai? Ta kai makamai da abinci, an ce bama-baman da aka jefa a Gaza ya fi yawan makamai da Amurka ta jefa a Afganistan.”
Ya ce taimako ba wani abu ba ne inda ya kiraye Musulmi kowa ya kawo taimakonsa inda ya ce Yahudawa ba abin amincewa ba ne.
Gumi ya bukaci Tinubu ya tube Wike a mukamin minista
A wani labarin, Sheikh Ahmed Gumi ya kira ministan Abuja, Nyesom Wike da shaidani inda ya bukaci Shugaba Tinubu ya kore shi.
Gumi ya bayyana haka ne yayin da ake zargin Wike na shirin rushe wani bangare na masallacin Abuja
Gumi ya ce tabbas idan aka ci gaba da haka to wannan gwamnati ba za ta tsallake shekaru hudu ba.
Asali: Legit.ng