Shugaban Amurka, Biden Ya Ba da Gudumawar Dala Miliyan 100 Ga Gaza

Shugaban Amurka, Biden Ya Ba da Gudumawar Dala Miliyan 100 Ga Gaza

  • Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, shugaban Amurka ya ba da gagarumar gudumawa
  • Joe Biden ya ba da Dala miliyan 100 na taimakon jin kai ga Gaza bayan farmakin da Isra’ila ke kai mata
  • Wannan na zuwa ne bayan Isra’ila ta kai farmaki mai muni a asibiti wanda ya halaka mutane fiye da 500

Gaza, Falasdinu – Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya ba da gudumawar Dala miliyan 100 don taimakawa Gaza.

Biden ya ba da taimakon ne bayan ya dira a yankin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra’ila da Kungiyar Hamas, cewar TheCable.

Shugaba Biden na Amurka ya ba da gudumawar Dala miliyan 100 ga Gaza
Shugaban Amurka, Biden Ya Ba da Gudumawar Kudi 100 Ga Gaza. Hoto: @JoeBiden.
Asali: Facebook

Wani gudumawa Biden na Amurka ya bai wa Gaza?

Shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba 18 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Biden Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Isra'ila Kan Harin da Aka Kai a Wani Asibiti a Zirin Gaza

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ina sanar da ba da gudumawar Dala miliyan 10 na jin kai ga Gaza da kuma West Bank.
"Wannan kudade za su taimakawa mutane miliyan daya da su ka rasa matsugunansu da kuma Falasdinawa wadanda wannan rikici ya shafa.
"Kuma za mu samar da wata hanya ta yadda za mu taimaka wa mabukata, amma ba kungiyar Hamas ko wasu kungiyar ta'addanci ba."

Legit Hausa ta tattauna da wasu kan wannan taimako na Biden:

Kabir Nuhu ya ce in shaa Allah lokacin Isra'ila ne ya zo ko sun kawo dauki ko ba su kawo ba.

Yayin da Hashim Abdullahi ya ce:

"Gaza ba ta bukatar wadannan kudade saboda azzalumi ne tun da ana kashe yara da mata kuma ya na goyon baya."

Aliyu Muhammad ya yi Allah wadai da wannan taimako inda ya ce me yasa ba sa goyon bayan Falasdinawa sai Isra'ila azzaluma.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Bi Umarnin Tinubu, Ta Tabbatar a Nadin Manyan Mukaman da Ya Tura

Meye matsayar Biden na Amurka kan Gaza, Isra'ila?

Bisa ga dukkan alamu kasar Amurka na goyon bayan ta'addanci da kasar Isra'ila ke yi kan Falasdinawa wanda ya sanadin rasa rayukan mutane da dama.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Joe Biden karara ya bayyana cewa ba Isra'ila ba ce ta kai hari kan asibiti da ya kashe mutane akalla 500.

Harin ya yi ajalin mutane da dama da su ka hada da mata da kananan yara da ke jinya a asibiti.

Amurka ta goyi bayan harin da Isra'ila ta kai Gaza

A wani labarin, shugaban Amurka, Joe Biden ya bayyana wadanda za su iya kai hari kan Gaza musamman wanda aka kai asibiti.

Biden yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa da alamu dayan bangaren ne su ka kai harin ba Isra'ila ba.

Harin da ake zargin Isra'ila ta kai kan asibiti ya hallaka mutane fiye da 500 wanda su ka hada da mata da yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.