Amurka Ta Goyi Bayan Isra'ila Kan Harin da Ta Kai a Wani Asibiti a Zirin Gaza
- Shugaban Amurka Joe Biden ya goyi bayan matsayar cewa harin da aka kai ranar Talata a wani asibiti a Gaza ba Isra'ila ce ta kai shi ba
- Biden ya ce bisa abin da ya gani na wannan mummunan lamari, ya bayyana a gare shi cewa "ɗayan ɓangaren" ne ke da alhakin harin
- Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron manema labarai a Tel Aviv tare da PM na Isra'ila, Benjamin Netanyahu a ranar Laraba, 18 ga Oktoba
Tel Aviv, Isra'ila - Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana waɗanda za su iya ɗaukar nauyin harin da aka kai wani asibiti a Gaza.
Biden ya ce dangane da abin da ya gani, harin da aka kai a asibitin ya yi kama da "ɗayan ɓangaren" ne ya kai harin bam ba Isra'ila ba, cewar rahoton Al Jazeera.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron manema labarai bayan ya isa birnin Tel Aviv babban birnin Isra'ila.
Ziyarar da shugaban na Amurka ya kai Isra'ila an ce ta kasance ta diflomasiyya domin hana yaƙin Gaza shiga wani rikici wanda zai shafin yankin Gabas ta Tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Biden ya samu tarba a filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke Tel Aviv daga hannun Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da shugaban ƙasar, Isaac Herzog a ranar Laraba 17 ga watan Oktoba.
Menene abin da Biden ya ce kan harin?
A kalamansa:
"Na yi baƙin ciki da kuma fusata da fashewar bam a asibitin Gaza a jiya, kuma bisa ga abin da na gani, ya zama kamar ɗayan ɓangaren ne suka yi, ba ku ba."
Amma akwai mutane da yawa a wajen, muna da abubuwa da yawa sannan akwai abubuwa masu yawa da muke son shawo kansu.
Biden ya ƙara da cewa:
"Duniya tana kallo. Isra'ila na da ƙimar da aka gindaya kamar yadda Amurka ke da ita, da sauran ƙasashen dimokuradiyya, kuma suna kallo domin ganin abin da za mu yi."
Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka
A wani labarin kuma, Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya yi Allah wadai da yaƙin da ake yi a zirin Gaza.
Sarkin Musulmin ya soki ƙasar Amurka kan yadda ta fito ƙarara tana nuna goyon bayan ta ga ƙasar Isra'ila a kisan gillar da take yi wa al'ummar Falasɗinawa.
Asali: Legit.ng