Tsohon Ministan Najeriya Ya Ce Israila Na Son Kitsa Yakin Duniya Na 3

Tsohon Ministan Najeriya Ya Ce Israila Na Son Kitsa Yakin Duniya Na 3

  • Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Farfesa Bolaji Akinyemi, ya bayyana cewa, Benjamin Netanyahu, firaministan ƙasar Isra'ila, na son ayi yaƙin duniya na uku
  • Akinyemi, a wata hira da ya aka yi da shi, ya ce shugaban na Isra’ila yana ƙoƙarin yin hakan ne ta hanyar haɗa Amurka da Iran faɗa
  • A ranar Lahadin da ta gabata ne Isra'ila ta shelanta yaƙi kan Falasdinu bayan wani hari da ƙungiyar Hamas da ke ɗauke da makamai ta Falasdinawa ta kai a kasarta

Farfesa Bolaji Akinyemi, tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, ya yi zargin cewa Benjamin Netanyahu, firaministan ƙasar Isra’ila, yana yunkurin kawo yaƙin duniya na uku.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE a ranar Talata 10 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Isra'ila Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ba Da Kariya Kan Rikicin Kasar Da Falasdinu, Ta Fadi Dalilai

Isra'ila na son kitsa yakin duniya na uku
Tsohon ministan Najeriya ya ce Isra'ila na son fara yakin duniya na uku Hoto: Benjamin Netanyahu
Asali: Twitter

Tsohon minista ya ce Isra'ila za ta fara yaƙin duniya na uku

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a yaƙin da ake cigaba da gwabzawa tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, kuma miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaƙi tsakanin Isra'ila Da Falasɗinu dai ya samo asali ne tun lokacin ƴan mulkin mallaka.

A ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba, Isra'ila ta shelanta yaƙi a zirin Gaza bayan wani hari da ƙungiyar Hamas ta kai wanda ba a taɓa ganin irinsa ba. Hankalin duniya ta karkata ga abin da zai biyo bayan hakan.

To sai dai a nasa martanin tsohon ministan na Najeriya kuma farfesa a fannin kimiyyar siyasa, ya ce firaministan Isra'ila, Netanyahu na shirin yin amfani da yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas wajen tayar da yaƙin duniya na uku ta hanyar haɗa Amurka da Iran faɗa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Sabon Nadin Mukami Mai Muhimmanci a Hukumar FCTA

Me farfesa Akinyemi ya ce kan yaƙin duniya na uku?

Farfesa Akinyemi ya bayyana cewa:

"Netanyahu yana ƙoƙarin fara yaƙin duniya na uku ta hanyar haɗa Amurka faɗa da Iran a wannan yakin idan har zai iya yin nasara. Kuma wannan shi ne shirinsa na ganin Amurka da Iran su yi fadan soji kai tsaye, to sai dai mu ce Allah ya taimake mu baki ɗaya."

FG Ta Magantu Kan Fadan Isra'ila Da Falasdinu

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta yi magana kan faɗan da ya ɓarke a tsakanin ƙasashen Isra'ila da Falasɗinu.

FG ta buƙaci ɓangarorin biyu da su tsagaita buɗe wuta sannan su koma kan teburin sulhu domin kawo ƙarshen rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng