Jerin Kasashen Afirka Da Ke Goyon Bayan Isra'ila Ko Falasdinawa, Da 'Yan Ba Ruwa Na

Jerin Kasashen Afirka Da Ke Goyon Bayan Isra'ila Ko Falasdinawa, Da 'Yan Ba Ruwa Na

Kasashen Nahiyar Afirka sun bambanta wurin goyon bayan daya daga cikin kasashen Isra'ila ko Falasdinu yayin da ake gwabza yaki.

An shafe kawanaki ana arangama tsakanin isra'ila da kuma 'yan kungiyar Hamas na Falasdinu.

Kasashen Afirka da ke goyon bayan Isra'ila ko Falasdinu
Ana gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Falasdinu. Hoto: Bola Tinubu/Cyril Ramaphosa/Nana Akufo Addo.
Asali: Facebook

Me ya jawo rikicin tsakanin isra'ila da Falasdinu?

Rikicin ya kara kamari ne bayan Isra'ila ta kai harin ramuwar gayya kan Falasdinu inda harin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma kananan yara.

Tun farko, kungiyar Hamas ta kai mummunan harin bazata na roka kan Isra'ila inda harin ya yi ajalin mutane da dama da raunata daruruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kasashe na kiran ayi sulhu don samun zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.

Amma wasu bangare kuma na kasashen na goyon bayan Isra'ila ko kuma Falasdinu.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Najeriya, Isra'ila da sauran kasashen da Amurka ba ta da jakadu da kuma dalili

Dan jarida a Nahiyar Afirka ta Yamma, Yusuf Akinlele ya wallafa a shafinsa na Twitter yadda kasashen su ka rarrabu kan rikicin.

Legit ta jero muku kasashen da kuma inda su ka karkata kan rikicin na Isra'ila da Falasdinu.

Kasashen Nahiyar Afirka da ke neman ayi sulhu

1. Najeriya

2. Masar

3. Kenya

4. Ghana

5. Morocco

6. Senegal

7. Tanzania

8. Uganda

Kasashen Nahiyar Afirka da ke goyon bayan Falasdinawa

1. Algeriya

2. Sudan

3. Tunisia

4. Afirka ta Kudu

5. Djibouti

Kasashen Nahiyar Afirka da ke goyon bayan Isra'ila

1. Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

2. Zambia.

A jiya Litinin 9 ga watan Oktoba, 'yan kungiyar Shi'a sun gudanar da tattaki don nuna goyon bayan Falasdinawa kan harin da Isra'ila ke kaiwa.

Kungiyar karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky sun bukaci hukumomi su dauki mataki kan Isra'ila saboda cin zarafin Falasdinawa.

Kara karanta wannan

Bayan naira triliyan 2.17, majalisar dattawa ta lamuncewa Tinubu ciyo bashin $7.8Bn da €100M

Isra'ila ta hallaka Falasdinawa 198 a harin ramuwar gayya

A wani labarin, Kasar Isra'ila ta kai farmaki a wani harin ramuwar gayya tare da hallaka Falasdinawa 198 bayan kungiyar Hamas ta kai musu hari.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar Hamas ta kai hari da makaman roka kan kasar isra'ila da ya yi ajalin mutane da dama.

Kasashen duniya da dama na kiran a koma teburin sulhu don tattaunawa da samun zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.