Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Rikicin Falasdinu-Israila

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Rikicin Falasdinu-Israila

  • Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga Isra'ila da Hamas da su tsagaita buɗe wuta tare da rungumar tattaunawa domin warware rikicin da ke faruwa a tsakanin ɓangarorin biyu
  • FG ta bayyana cewa rikicin da ke cigaba da faruwa zai samar da wani yanayi mara daɗi da wahala ga fararen hula daga ɓangarorin biyu
  • Rikicin Gaza- Isra'ila wani ɓangare ne na rikicin Isra'ila-Falasɗinu a cikin gida amma kuma wani wuri ne da ake gwabza faɗa tsakanin manyan ƙasashen yankin

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana matuƙar damuwarta game da ɓarkewar rikici tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu, da sanyin safiyar Asabar, 7 ga watan Oktoba.

Gwamnatin Najeriya a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun ministan harkokin ƙasashen waje, Yusuf Tuggar, ta yi kira da a sassauta rikicin tare da tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna.

Kara karanta wannan

Kungiyar Hamas Ta Falasdinu Ta Kai Mummunan Hari a Isra'ila

FG ta yi magana kan rikicin Falasdinu-Isra'ila
Gwamnatin tarayyya ta bukaci bangarorin biyu su tsagaita wuta Hoto: Amir Levy, Nigerian Presidency/Handout/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

'Ku yi aiki da tattaunawa', Najeriya ga Isra'ila, Falasɗinu

Gwamnatin Bola Tinubu ta buƙaci ɓangarorin biyu da su ba da dama domin bayar da taimakon jin ƙai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni gwamnatocin Indiya da Amurka suka mayar da martani kan halin da ake ciki a Gaza.

Wani ɓangare sanarwar na cewa:

"Cigaba da rikici da ramuwar gayya da ke aukuwa a halin yanzu, babu abin da zai jawo face wahala ga fararen hula waɗanda a koda yaushe rikicin a kansu yake ƙarewa."
"Domin haka gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga ɓangarorin biyu da su yi hakuri, su ba da fifikon kare lafiyar fararen hula da kuma ba da damar kula da ayyukan jin ƙai."
"Domin haka muna kira da a warware rikicin cikin lumana ta hanyar tattaunawa.”

Isra'ila Ta Halaka Falasdinawa 198

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Isra'ila ta ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan al'ummar Falasɗinawa, bayan ƙungiyar Hamas mai rajin kare Falasɗinawa ta kai hari a Isra'ila.

Harin na ramuwar gayyya wanda Isra'ila ta ƙaddamar a zirin Gaza s ranar Asabar, 7 ga watan Oktoban 2023, ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 198 yayin da wasu da dama suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng