Ghana Za Ta Taimakawa Najeriya Da Wutar Lantarki Bayan Samun Matsala A Kasar
- Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Ghana ta yi alkawarin taimakawa Najeriya da wutar lantarki
- Kasar ta ce za ta taimakawa Najeriya wurin tabbatar da samun kaso 100 na karfin wutar lantarki a duniya
- Shugaban hukumar, Henson Monney shi ya bayyana haka a jihar Legas yayin taron makamashi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Accra, Ghana - Kasar Ghana ta shirya taimakon Najeriya da wutar lantarki ganin yadda kasar ke fama da wannan matsala.
Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a Ghana, Henson Monney shi ya bayyana haka yayin wani taro a jihar Legas, Legit ta tattaro.
Da meye Ghana ke shirin taimakon Najeriya da shi?
Ya ce Ghana ta cika kaso 80 zuwa 85 na karfin wutar lantarki saboda tsare-tsare masu kyau.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kasar na son taimakawa Najeriya ta samu kaso 100 na karfin wutar lantarki a duniya.
Ya ce da zarar Najeriya ta gyara matsalolin wutar lantarki a kasar, Ghana za ta fara taimaka mata da wutar.
Najeriya na fama da matsalar wutar lantarki sama da shekaru 50 wanda gwamnatoci da dama su ka gagara shawo kan matsalar
Meye dalilin taimakawa Najeriya da Ghana ke shirin yi?
Wannan na zuwa ne bayan kasar Najeriya ta samu lalacewar wutar lantarki har sau biyu a cikin mako guda, cewar Nairametrics.
An shafe shekara daya ba tare da samun irin wannan matsala ba tun lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Duk da matsalar wutar a kasar, Najeriya ta yanke wutar da ta ke taimakawa Jamhuriyar Nijar saboda matsalar diflomasiyya a tsakanin kasashen.
Najeriya ta dauki matakin ne bayan hambarar da Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar a ranar 26 ga watan Yuli da sojoji su ka yi.
An dauke wutar lantarki gaba daya a Najeriya
A wani labarin, a karon farko cikin shekara daya, an dauke wutar lantarki a fadin Najeriya baki daya a safiyar Alhamis 14 ga watan Satumba.
Kamfanin samar da wutar a Najeriya (TCN) ya tabbatar da lalacewar wutar lantarki a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis 14 ga watan Satumba.
Wannan shi ne karon farko a cikin shekara daya da aka dauke wutar lantarki gaba daya a Najeriya tun bayan daukewarta a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Buhari.
Asali: Legit.ng