Hambararren Shugaban Kasar Gabon Ali Bongo Ya Shaƙi Iskar 'Yanci
- Sojojin ƙasar Gabon sun saki hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo bayan shafe kwanaki bakwai a tsare
- Sun bayyana cewa yana da ikon zuwa duk inda ya ga dama a duniya domin neman maganin rashin lafiyar da ke damunsa
- Mulkin Ali Bongo dai ya zo ƙarshe ne a ranar Laraba, 30 ga watan Agustan da ya gabata
Libreville, ƙasar Gabon - Sojojin juyin mulkin ƙasar Gabon, sun bayyana sakin hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo, kwanaki bakwai bayan kifar da gwamnatinsa.
Shugaban mulkin sojin ƙasar, Brice Oligui Nguema ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi na sa da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar.
Sojojin dai sun kifar da gwamnatin Bongo ta tsawon shekaru 14, a ranar Laraba, 30 ga watan Agustan da ya gabata kamar yadda Channels TV ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun bai wa hamɓararren shugaban Gabon 'yanci fita ƙasar
Sanarwar ta Nguema ta bayyana cewa Ali Bongo na da 'yancin zuwa duk inda ya ga dama, ciki kuwa har da fita zuwa ƙasashen ƙetare.
Da yake karanto jawaban shugaban mulkin sojin, Kanar Ulrich Manfoumbi Manfoumbi ya ƙara da cewa Ali Bongo ba da damar tafiya ƙasar waje domin neman magana rashin lafiyar da yake fama da ita.
Ali Bongo ya yi fama da matsananciyar shanyewar jiki a watan Oktoban 2018, wanda hakan ya sa ya samu nakasu, ta yadda yake shan wahala wajen motsa kafa da hannunsa ɗaya.
Shugabancin Ali Bongo a Gabon
Hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo, ya samu damar ɗarewa kan karagar mulkin ne bayan mutuwar mahaifinsa da ya shekara 41 kan mulki wato Omar Bongo, a shekarar 2009.
An sake zaɓar Ali Bongo a karo na biyu a shekarar 2016, sai dai bayan shekaru biyu ne ya gamu da matsalar ciwon shanyewar jiki kamar yadda Africa News ta ruwaito.
An bayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙasar na 2023 da aka yi mai cike da rikici, inda aka ce ya samu kaso 64.27%, yayin da abokin hamayyarsa Ondo Ossa, ya samu 30.77%.
Sai dai jim kaɗan bayan ayyana Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓen ne sojojin ƙasar suka sanar da yin juyin mulki.
Ruwanda da Kamaru sun yi wa jami'an tsaronsu garambawul
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sauye-sauyen da kasashen Ruwanda da Kamaru suka yi wa sojojin kasarsu biyo bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar Gabon.
Shugabannin kasashen Afrika da dama sun shiga cikin firgici biyo bayan kwace mulkin Ali Bongo da sojoji suka yi a ƙasar ta Gabon.
Asali: Legit.ng