Sojojin Faransa Sun Fara Tattaunawa Da Sojin Jamhuriyar Nijar Kan Ficewarsu Daga Kasar
- Dangantaka na kara kamari tsakanin kasar Faransa da Jamhuriyar Nijar tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum
- A makon da ya gabata, sojojin Jamhuriyar Nijar sun bukaci sojin kasar Faransa su fice musu daga kasa cikin gaggawa
- Sai dai a yanzu sojojin na Faransa sun fara tattaunawa da Nijar don taimaka musu su janye a hankali ba tare da tashin hankali ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yamai, Nijar - Rahotanni a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa an fara tattaunawa da sojojin Faransa.
An tabbatar cewa sojojin Faransa na tattaunawa da takwarorinsu a Nijar don saukaka musu yadda za su janye sojojinsu a hankali.
Meye ya jawo matakin Nijar kan Faransa?
Wannan na zuwa ne bayan sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ba da umarni ga sojojin Faransa da su fice daga kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da sojojin Faransa ke neman hanyar janye kayayyakin aikinsu cikin lumana kamar yadda shugabannin juyin mulki su ka bukata, cewar DW.
Fira Ministan Nijar, Lamine Zeine ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da juna don ganin yadda sojojin Faransa za su janye daga kasar cikin gaggawa.
Nawa ne adadin sojin Faransa a Nijar?
Kasar Faransa na da sojojin kimanin 1,500 a Nijar don taimakawa wurin yaki da masu ikirarin jihadi, kamar yadda RFI ta tattaro.
Sai dai wannan dangantaka ta fara samun tsaiko tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.
Matsalar ta fara ne bayan Faransa ta ci gaba da goyon bayan hambararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum bayan kifar da shi a watan Yulin.
Faransa ita ce ta reni Jamhuriyar Nijar lokacin mulkin mallaka kafin samun 'yancin kai a kasar.
Kamfanonin Faransa Sun Yi Asara Bayan Juyin Mulki A Gabon
A wani labarin, bayan kifar da gwamnatin Ali Bongo a kasar Gabon, Faransa ta tafka mummunan asara a kasar bayan kamfanoninta uku sun tafka mummunan asara na hannun jari.
Rahotanni sun tabbatar cewa an samu matsala yayin da hannayen jari a manyan kamfanonin Faransa guda uku sun fadi a kasuwar hada-hadar hannun jari ta Paris.
Idan ba a mantaba a makon da ya gabata sojojin kasar Gabon sun kifar da gwamnati Ali Bongo bayan shafe shekaru 12 ya na mulkin kasar.
Asali: Legit.ng