"Mu Makota Ne" Shugaba Tinubu Ya Bude Gaskiya Kan Yaki da Sojojin Jamhuriyar Nijar

"Mu Makota Ne" Shugaba Tinubu Ya Bude Gaskiya Kan Yaki da Sojojin Jamhuriyar Nijar

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce yana ta fargabar cewa sojoji za su fara karbe mulki a Afrika bayan juyin mulkin Nijar, inda ya yi misali da Gabon
  • Yayin da yake jawabi ga tawagar sulhu na Sarkin Musulmi a kasar da ke makwabtaka, shugaban kasar ya nanata cewa ba abun yarda bane hambarar da gwamnatin damokradiyya
  • A cewar shugaban kasar, kowa zai ji a jikinsa idan Najeriya ta bari abun da ya faru a Nijar ya dawwama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa tsoron da ya dunga ji game da juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar ya tabbata da abun da ya faru a Gabon inda sojoji suka tsige Shugaba Ali Bongo ta hanyar kifar da gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya ce ya yi fargabar cewa matakin da sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar suka dauka zai kafa mummunan tarihi ga nahiyar bakar fata. Fadar shugaban kasa ta bayyana haka a cikin wata wallafa a manhajar X.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

Tawagar sulhu karkashin jagorancin Sarkin Musulmi tare da shugaban kasa
“Tsorona Ya Zama Gaskiya”: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Shugaban kasa Tinubu yana tsoron yaduwar juyin mulkin soji a fadin Afrika

Gabon ce kasar Afrika da sojoji suka yi juyin mulki a baya-bayan nan bayan wasu manyan janar na rundunar soji sun sanar da kwace mulki a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nan take masu juyin mulkin suka soke zaben da aka yi a kwanan nan sannan suka kawo karshen gwamnatin Bongo ta shekaru 13. Ya gaji mulki a 2009 daga mahaifinsa wanda ya shugabanci kasar tsawon shekaru 40.

Sai dai kuma, a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, Shugaban kasa Tinubu ya bayyana tsoronsa lokacin da ya karbi ba kuncin tawagar Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Tinubu ya yi alkawarin binciko duk wata hanyar diflomasiya don kafa dimokradiyya a Nijar

Kara karanta wannan

Fargabar Juyin Mulki: Rwanda, Kamaru Sun Dauki Tsauraran Matakai Kan Rundunar Tsaronsu, Sun Bayyana Matakan

A cewar shugaban kasar, za a bincika duk wata kofar diflomasiyya tare da masu juyin mulki a Jamhuriyar Nijar kafin daukar matakin amfani da sojoji a matsayin mafita na karshe.

Tinubu ya dage cewa cire gwamnatin damokradiyya ta karfi ba abu ne da za a yarda da shi ba har abada.

"Dole nayi muku godiya saboda ziyara da dama da kuka kai Jamhuriyar Nijar, Masu martaba, amma ya zama dole ku sake komawa. Tsorona ya tabbata a Gabon cewa masu kwaikwayo za su fara aikata irin haka har sai an dakatar da shi. Mu makwabta ne da Jamhuriyar Nijar, kuma abin da ya hada yan Najeriya da manyan mutanensu ba abu ne da za iya rabawa ba. Babu wanda ke sha'awar yaki. Mun ga irin barnar da aka yi a Ukraine da Sudan. Amma, idan ba mu tufkar hanci ba, gaba dayanmu za mu fuskanci sakamakon tare."

Kara karanta wannan

Ku kama kanku: Kungiyar AU ta fusata da juyin mulkin Gabon, ta gargadi sojoji

Atiku ya yi martani kan juyin mulkin sojoji a Nijar

A wani labarin, mun ji cewa Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon, kasar da ke Afrika ta tsakiya.

A wata wallafa da ya yi a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwa game da yawan juyin mulki da sojoji ke yi a Afrika, cewa ya kamata nahiyar ta mayar da hankali wajen magance cutar maimakon alamunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng