Juyin Mulki: Kungiyar AU Ta Dakatar Da Gabon Daga Cikin Mambobinta
- Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta dakatar da ƙasar Gabon daga cikin mambobinta
- Kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na gaggawa
- Hakan ya biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi wa shugaban ƙasar Ali Bongo a makon da ya gabata
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika (AU), ya sanar da dakatar da ƙasar Gabon daga cikin mambobin kungiyar biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi.
Sanarwar dai ta fito ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, a cikin wani saƙo da aka wallafa a shafin kwamitin na X.
Dalilin kungiyar AU na dakatar da ƙasar Gabon
Ƙungiyar ta tarayyar Afrika ta kuma yi Allah wadai da ƙwace mulki da sojojin ƙasar ta Gabon suka yi daga hannun hamɓararren shugaban wato Ali Bongo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
AU ta ce dakatarwar da aka yi wa Gabon ta shafi duk wasu hulɗoɗi da sauran 'yan kungiyar ke iya mora, sannan kuma ba za a maido ta ba har sai lokacin da sojoji suka mayar da mulki hannun farar hula.
Hakan na zuwa ne bayan dakatarwa da ƙungiyar ta yi wa jamhuriyar Nijar biyo bayan kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum da sojin ƙasar suka yi a kwanakin baya.
Juyin mulkin ƙasar ta Gabon da ya wakana, ya kawo ƙarshen mulkin da ake wa kallon kamar na gado da tsatson su Ali Bongo suka shafe kusan shekaru 60 suna yi kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Ƙungiyar AU ta goyi bayan ECOWAS kan tura dakaru Nijar
A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa a kwanakin baya, ƙungiyar tarayyar Afrika (AU), ta nuna goyon bayanta ga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) na matakin tura dakaru Nijar.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa a shirye take ta taimakawa da ƙungiyar ta ECOWAS a duk lokacin da ɓuƙatar hakan ta taso.
Shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat ne ya bayyana hakan a wani taro.
Tinubu ya ce abinda yake tsoro ya tabbata a juyin mulkin Gabon
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kalaman da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi na cewa fargabar da yake da ita bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar ta tabbata a Gabon.
Ya ce ya yi hasashen cewa juyin mulkin na Nijar zai janyo sojojin wasu ƙasashen na Afrika su yi sha'awar kifar da gwamnatocin ƙasashensu.
Asali: Legit.ng