Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Shugaba Ali Bongo Na Kasar Gabon

Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Shugaba Ali Bongo Na Kasar Gabon

  • Ƙasar Gabon ta koma ƙasa ta takwas a nahiyar Afirika da ta koma ƙarƙashin mulkin soja a cikin ƙarni na 21, bayan sojoji sun karɓe mulki a ranar Laraba
  • Juyin mulkin na zuwa ne bayan an sanar da sakamakon zaɓen ƙasar na ranar Asabar, wanda Shugaba Ali Bongo ya lashe a karo na uku
  • Ahalin Bongo sun mulki ƙasar Gabon har na tsawon shekara 53, bayan ya karɓi mulki a hannun mahaifinsa wanda ya kwashe shekara 40 a kan karagar mulki

Kasar Gabon - Sojoji sun sanar da hamɓarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo na ƙasar Gabon, wanda ya lashe zaɓen da aka yi na shugaban ƙasa a ranar Asabar, 26 ga watan Agusta.

Bongo, wanda ya hau kan mulki bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 2009, ya lashe zaɓe karo na uku, a zaɓen da ƴan adawa suka ce an tafka maguɗi.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Jerin Kasashen Afrika 7 Da Ke Karkashin Mulkin Soji Yayin Da Sojoji Suka Karbe Karin Wata Kasar

Sojoji sun yi juyin mulki a Gabon
Sojoji sun sanar da yin juyin mulki a Gabon Hoto: Malkolm M./Afrikimages Agency/Universal Images Group, DESIREY MINKOH/AFP
Asali: Getty Images

Jaridar BBC ta ambato sojojin sun bayyana a gaban gidan talabijin na ƙasar Gabon inda suka sanar da cewa sun ƙarɓe mulki.

Sojojin juyin mulkin sun kuma sanar da soke zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kawo ƙarshen mulkin Ali Bongo

Juyin mulkin ya kawo ƙarshen shekara 53 da ahalin Bongo suka kwashe suna kan madafun ikon ƙasar Gabon.

A cikin sanarwar da sojojin suka fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, sun sanar da soke zaɓen shugaban ƙasar wanda suka ce ba sahihi ba ne, rahoton Aljazeera ya tabbatar.

Sojojin sun kuma sanar da cewa sun soke dukkanin wasu ma'aikatun gwamnati, tare da kulle gaba ɗaya iyakokin ƙasar.

Wannan juyin mulkin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin warware rikicin hamɓarar da gwamnatin Shugaba Bazoum da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

Ƙungiyoyin raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) da tarayyar Afirika (AU), wanɗanda suka yi fatali da juyin mulkin Nijar, ba su ce komai ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Sojoji Sun Hambarar Da Gwamnatin Bazoum

A baya rahoto ya zo cewa, sojoji a Jamhuriyar Nijar sun sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

Sojojin sun bayyana cewa sun hamɓarar da gwamnatin Shugaɓa Bazoum ne saboda rashin tsaro da rashin kyawun shugabanci a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng