Juyin Mulki: Manyan Abubuwa 5 Da Suka Faru Kan Rikincin Jamhuriyar Nijar

Juyin Mulki: Manyan Abubuwa 5 Da Suka Faru Kan Rikincin Jamhuriyar Nijar

Tun bayan sanar da hamɓarar da tsohon shugaban Nijar Mohamed Bazoum da shugaban sojojin juyin mulkin Nijar Abdourahmane Tchiani ya jagoranta, abubuwa da dama sun wakana a ciki da wajen ƙasar.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin juyin mulkin umarnin su mayarwa da tsohon shugaban ƙasar kujerarsa ko su fuskanci mummunan mataki.

An samu masu shiga tsakanin da dama da ke ƙorarin ganin an sasanta rikicin cikin lalama, wanda a cikin hakan ne Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin manyan abubuwa biyar da suka wakana a makon da muke ciki.

Abubuwan da suka wakana kan jamhuriyar Nijar
Manyan abubuwa 5 da suka wakana kan rikicin jamhuriyar Nijar. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Ganawa da malaman addinin Musulunci

A ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta ne dai Shugaba Bola Tinubu ya gana da tawagar malaman addinin Musulunci a fadarsa da ke birnin tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ba Zai Yiwu Ba": Sojojin Nijar Sun Bayyana Dalilin Kin Dawo Da Bazoum Kan Mulki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana cewa malaman sun gana da Tinubu ne domin ba shi bayani kan ziyarar da suka kai jamhuriyar Nijar kamar yadda Vanguard ta wallafa.

AU ta dakatar da Nijar daga cikin mambobinta

A cikin makon nan ne Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta sanar da dakatar da jamhuriyar Nijar daga cikin mambobinta.

Ƙungiyar ta AU ta ce ba za ta mayar da Nijar cikin mambobinta ba har sai lokacin da ƙasar ta koma turbar dimokuraɗiyya kamar yadda Channels TV ta wallafa.

Maganar sojoji kan mayar da Bazoum kan mulki

A cikin makon nan ne dai jagoran masu shiga tsakanin na kungiyar ECOWAS, Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa sojojin Nijar sun ce ba za su mayar da Bazoum kan kujerarsa ba.

Abdulsalami ya ce sojojin sun faɗa ma sa cewa a shirye suke su yi kowace irin tattaunawa da ECOWAS, amma banda batun mayar mulki hannun farar hula.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: "Ku Tsaya Cikin Shiri", Sojojin Nijar Sun Tura Muhimmin Sako Ga Dakarunsu Yayin Da ECOWAS Ke Shirin Afka Musu

Kulla ƙawancen soji tsakanin Nijar, Mali da Burkina Faso

Shugabannin mulkin sojin jamhuriyar Nijar sun sanar da ƙulla ƙawance na soji tsakaninsu da ƙasasehen Mali da Burkina Faso ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta a Yamai babban birnin ƙasar.

Ƙawance zai bai wa duka ƙasashen uku damar taimakawa junansu a duk lokacin da aka kai wa ɗaya daga cikinsu hari da kuma sauran matsaloli na tsaro.

An fama da ƙarancin dabbobi saboda rufe iyakoki

Wani rahoto da Legit.ng ta wallafa a baya ya nuna yadda al'umma musamman ma waɗanda ke kasuwancinsu a kan iyakokin Najeriya da Nijar ke ci gaba da kokawa.

'Yan kasuwar shanu da ke kan iyakokin sun bayyana yadda adadin shanun da suke sayarwa da waɗanda suke yankawa ya ragu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Egypt da Algeria sun ki amincewa da amfani da ƙarfin soji kan Nijar

Kara karanta wannan

Za a yi ta: Faransa ta daga yatsa ga sojin Nijar bayan umarnin korar jakadanta a kasar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ƙin amincewa da ƙasashen Egypt da Algeria suka yi kan amfani da matakin soji wajen dawo da dimokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar.

A yayin da kungiyar ECOWAS ke nuna alamu kan yiwuwar amfani da mataki na soji wajen shawo kan rikicin na Nijar, ƙasashen biyu sun ce zama kan teburin sulhu ya fi dacewa a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng