"439k Duk Wata": Yar Najeriya Ta Nunawa Duniya Daki 1 Da Ake Biyan Miliyan 5.2 Duk Shekara a UK

"439k Duk Wata": Yar Najeriya Ta Nunawa Duniya Daki 1 Da Ake Biyan Miliyan 5.2 Duk Shekara a UK

  • Wata matashiyar budurwa da ke zaune a UK ta nunawa duniya wani daki da ake biyan kudin haya N439k duk wata, sannan ta saki bidiyon dakin
  • Gidan mai daki daya yana a wajen Newcastle, kasar Birtaniya, sannan matashiyar ta zagaya cikin dakin don duba yadda yake
  • Wasu masu amfani da TikTok sun ce dakin ya yi arha a kan N439k wanda ke nufin yan haya za su biya miliyan 5.2 duk shekara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya da ke zaune a kasar Birtaniya ta wallafa wani bidiyo da ke nuna gidan da za a ba da haya N439k duk wata.

Gidan mai daki daya ne da ke a wajen Newcastle kuma Dat Naija Girl ta dauki bidiyon yadda fasalin gidan yake sannan ta wallafa shi a intanet.

Matashiya da ke zaune a UK ta baje kolin dakinta
"439k Duk Wata": Yar Najeriya Ta Nunawa Duniya Daki 1 Da Take Biyan Miliyan 5.2 a Shekara a Bidiyo Hoto: TikTok/@datnaijagirll.
Asali: TikTok

Fasalin cikin gidan N439k duk wata a Newcastle, UK

Kara karanta wannan

“Tana Biyan 238k Duk Wata”: Yar Najeriya Ta Baje Kolin Dakinta a Kasar Japan, Bidiyon Ya Yadu

Matashiyar ta zagaya da masu kallonta domin su ga cikin dakin, tana mai nuna yadda aka tsara cikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta nuno cikin dakin, kicin, bandaki da wajen wanka a cikin dakin.

Duk mai son karbar hayar gidan mai daki daya a Newcastle zai dunga biyan zunzurutun kudi har naira miliyan 5.2 duk shekara.

Lokacin da ta wallafa bidiyon, ya haddasa cece-kuce a tsakanin mabiyanta. Wasu sun dage cewa dakin ya yi arha kuma ya ci kudinsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga bidiyon daki daya a Newcastle, UK

@thistemmy ta ce:

"Wannan gidan zai kai 1300 a Landan."

@Obinna John Egbuniwe ya yi martani:

"Shiyasa ya yi arha. Wannan zai kai kamar £1,200 duk wata a Landan."

@Chinenye Berny-Amore ta ce:

" Na biya £850 kan abu makamancin wannan a East Sussex."

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

@Damilola Marshal ta yi martani:

"Baaba na sha wahala a Landan dinnan. Ina so na bar Landan dinnan."

Yar Najeriya ta baje kolin dakinta a kasar Japan

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wata matashiya yar Najeriya, Prospee, ta baje kolin dakinta na kasar Japan, wanda take biyan $309 (kimanin N238k) duk wata a matsayin kudin haya.

Baya ga intanet mara yankewa, ta bayyana cewa dakin nata ya zo da gado, talbijin, na'urar dumama abinci, firinji, na'urar sanyaya wuri da injin wanki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng