Matukin Jirgin Sama Ya Mutu a Bandaki Yayin Da Jirgin Ke Gudu a Sararin Samaniya

Matukin Jirgin Sama Ya Mutu a Bandaki Yayin Da Jirgin Ke Gudu a Sararin Samaniya

  • Fasinjojin cikin wani jirgi da ya taso daga birnin Miami zuwa Chile sun gamu da tashin hankali
  • Matuƙin jirgin mai ɗauke da mutane 271 ne ya yanke jiki ya faɗi a yayin da ake sheƙa gudu
  • Sai dai sun samu taimakon Ubangiji, yayinda abokan aikinsa suka saukar da jirgin zuwa ƙasa cikin gaggawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani abu na tashin hankali ya faru da fasinjojin jirgin sama 271 da suka taso daga Miami zuwa Chile, inda matauƙin jirginsu ya yanke jiki ya faɗi matacce a yayin da ake sheƙa gudu a sararin samaniya.

Matuƙin wanda aka bayyana sunansa da Ivan Andaur, ya fara jin alamar rashin lafiya bayan sa'o'i uku da tashin jirgin na kamfanin LATAM daga Florida zuwa Santiago.

Matuƙin jirgin sama ya mutu ana cikin tafiya
Matuƙin jirgin sama ya rasu ana tsaka da tafiya a sararin samaniya. Hoto: A Fly Guy's Cabin Crew Lounge
Asali: Facebook

Matuƙin jirgin sama ya yanke jiki ya faɗi a banɗaki

Kara karanta wannan

Wike: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Gameda Ministan Tinubu Na Birnin Tarayya

Bayan alamomin ciwon da ya ji a jikinsa, Ivan ya yanke jiki ya faɗi a banɗakin cikin jirgin, inda daga nan ne aka ba shi agaji na gaggawa, kuma aka ci gaba da tafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan shafe mintoci 30 a sararin samaniya, jirgin ya yi saukar gaggawa a wani filin jirgin sama da ke birnin Panama, inda a nan ne aka tabbatar da rasuwar Ivan mai shekaru 25 kamar yadda Independent ta ruwaito.

Jirgin mai lamba LA505 ƙirar Boeing 787-9, ya taso ne daga birnin Miami da misalin ƙarfe 10.11 na daren ranar Litinin, 14 ga watan Agustan shekarar 2023 kamar yadda India Today ta wallafa.

An kama fasinjan jirgin sama kan satar naira miliyan ɗaya

A wani labarin ba daban da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun ji yadda aka kama wani fasinjan jirgin sama da ya ƙware a sata a cikin jirgi.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba 'Yan Najeriya Haƙuri, Ya Fadi Sabbin Matakan Rage Raɗaɗin Da Ya Dauka

An kama fasinjan kan satar naira miliyan ɗaya, da kuma satar kwamfutar tafi da gidanka a cikin jakar wani fasinjan.

Lamarin ya faru ne a cikin wan jirgin jigilar fasinja na kamfanin Air Peace, da ya tashi daga Abuja zuwa birnin Patakwal.

Jirgin sama ɗauke da fasinjoji ya yi saukar gaggawa a Abuja

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan saukar gaggawar da wani jirgin sama mallakin kamfanin Aero Contractors ya yi a Abuja babban birnin tarayya.

An bayyana cewa jirgin ya yi saukar gaggawar ne mintuna kaɗan da tashinsa daga Abuja zuwa Patakwal da ke jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng