Shugabannin Rundunonin Tsaron ECOWAS Sun Ce A Shirye Suke Su Kai Hari Jamhuriyar Nijar

Shugabannin Rundunonin Tsaron ECOWAS Sun Ce A Shirye Suke Su Kai Hari Jamhuriyar Nijar

  • Shugabannin rundunonin tsaron ECOWAS sun ce shirye suke su kai hari Nijar
  • Sun bayyana hakan ne a wajen taron shugabannin rundunonin tsaron da ya wakana a ƙasar Ghana
  • Dakarun sun nuna yadda suka ƙosa su ga an dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Accra, Ghana - Shugabannin rundunonin tsaron kungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), sun ce a shirye suke su yaƙi sojojin jamhuriyar Nijar.

Sun bayyana hakan ne a wajen taron da suka gudanar a Accra babban birnin kasar Ghana a ranar Alhamis 17 ga watan Agusta kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ta ECOWAS ke ƙoƙarin ganin ta dawo da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojojin Nijar suka kifar a watan Yuli.

Kara karanta wannan

ECOWAS Ta Shawarci Sojojin Juyin Mulkin Nijar Bayan Wani Hari Da 'Yan Bindiga Suka Kai Mu Su

Dakarun ECOWAS sun shirya kai hari Nijar
Shugabannin rundunonin tsaron ECOWAS sun shirya kai hari jamhuriyar Nijar. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

ECOWAS ta ce a shirye ƙasashenta suke su yaƙi sojojin Nijar

Kungiyar ta ECOWAS ta bayyana cewa da yawa daga cikin ƙasashenta sun shirya domin shiga cikin wannan yaƙi na ƙwato mulki hannun sojin Nijar kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana cewa ƙasashen da ke a ƙarƙashin mulkin soji ne kawai da kuma ƙasar Cape Verde ba su amince da ƙwaci mulkin hannun sojojin Nijar ba.

Kwamishinan harkokin siyasa, tsaro da zaman lafiya na ECOWAS Abdel-Fatau Musah, ya ce za su je Nijar su ƙwaci mulkin da ƙarfi muddun sojojin ƙasar suka ki yin sulhu da su.

Mali da Burkina Faso ba su yadda a kai hari Nijar ba

Ƙasashen Mali da Burkina Faso, waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji, sun bayyana cewa za su taimakawa jamhuriyar Nijar muddun ƙungiyar ECOWAS ta yi yunƙurin kai ma ta hari.

Kara karanta wannan

Shugabannnin Rundunonin ECOWAS Za Su Yi Taro Dangane Da Umarnin Ɗamarar Yaƙi Da Sojojin Nijar Da Aka Ba Su

Ƙasar Guinea wacce ita ma sojoji ne ke mulkarta a halin da ake ciki, ta nuna adawarta da amfani da ƙarfi wajen ƙwatar mulki hannun sojojin juyin mulkin Nijar.

Sai dai masana harkokin tsaro sun nuna cewa ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU), za ta iya dakatar da ƙungiyar ECOWAS daga kai hari Nijar idan ya zamto hakan zai jefa yankin Afrika cikin fitina.

Putin ya buƙaci a sasanta rikicin Nijar cikin lumana

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shawarar da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya bayar dangane da rikicin jamhuriyar Nijar.

Putin a yayin da yake zantawa da shugaban mulkin soji na ƙasar Mali, ya buƙaci a sasanta rikicin na Nijar cikin lumana ba tare da yin amfani da bakin bindiga ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng