Shugabannin Rundunonin ECOWAS Za Su Yi Taro Don Duba Yiwuwar Amfani Da Karfi Wajen Ƙwatar Mulki a Nijar

Shugabannin Rundunonin ECOWAS Za Su Yi Taro Don Duba Yiwuwar Amfani Da Karfi Wajen Ƙwatar Mulki a Nijar

  • Shugabannin rundunonin tsaro na ECOWAS, sun tsaida ranar da za su sake zama kan batun jamhuriyar Nijar
  • Shugabannin za su gudanar da taron ne a cikin makon nan a birnin Accra da ke ƙasar Ghana
  • Tun a satin da ya gabata ne dai shugabannin rundunonin tsaron suka so gabatar da taron

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugabannin rundunonin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS, za su yi taro a ƙasar Ghana cikin satin da muke ciki.

Tun satin da ya gabata ne suka so yin taron, wanda aka ɗaga biyo bayan umarnin ɗaura ɗamarar yaƙi da Nijar da ECOWAS ta ba su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugabannin rundunonin tsaron ECOWAS za su yi taro a Ghana
Shugabannin rundunonin tsaro na ECOWAS za su yi taro don duba yiwuwar amfani da ƙarfin soji. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shugabannin Rundunonin ECOWAS sun faɗi ranar da za su yi taro na gaba

Biyo bayan ɗage taron da shugabannin rundunonin tsaron na ECOWAS suka yi a satin da ya gabata, sun tsaida ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar da za su yi taro don yanke shawara kan Nijar.

Kara karanta wannan

Abinda Sakataren Amurka Ya Faɗawa Tinubu Kan ECOWAS Dangane Da Juyin Mulkin Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za su yi taron ne a Accra, babban birnin ƙasar Ghana domin duba yiwuwar amfani da ƙarfin soji wajen ƙwatar mulkin daga hannun sojojin Nijar.

Kungiyar ECOWAS dai na neman sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar da su miƙa mulkin cikin ruwan sanyi ko kuma su fuskanci mataki mai tsauri kamar yadda The Guardian ta wallafa.

An samu rabuwar kai cikin ECOWAS kan tura dakaru Nijar

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan rabuwar kawunan da aka samu tsakanin 'yan majalisar ECOWAS dangane da batun tura dakarun soji jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin 'yan majalisar ta ECOWAS sun nuna amincewarsu kan tura dakarun soji Nijar domin su ƙwaci mulki da ƙarfi.

Wasu kuma daga cikin 'yan majalisar ba su amince da amfani da ƙarfi ba, inda suke ganin cewa hakan zai iya janyo ƙarin rincaɓewar al'amura a yankin Afrika ta Yamma.

Kara karanta wannan

Firaministan Nijar Ya Fadi Abinda Za Su Yi Dangane Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mu Su

Kungiyar AU ta goyi bayan ECOWAS kan tura dakaru Nijar

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan goyon bayan da kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta nunawa ƙungiyar ECOWAS, wajen ganin an dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijar.

Kungiyar ta AU ta yi alƙawarin taimakawa ƙungiyar ECOWAS a ƙoƙarinta na ganin mulkin ya koma hannun Bazoum da sojoji suka yi wa juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng