An Dage Gudanar Da Taron Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS
- An ɗage gudanar da taron manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS)
- An shirya gudanar da taron ne domin samar da hanyoyin da za a bi wajen yin amfani da sojojin ko-ta-kwana na ƙungiyar a Nijar
- Sai dai, an ɗage gudanar da taron wanda da aka shirya gudanarwa a birnin Accra na ƙasar Ghana har sai abinda hali ya yi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Taron manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) da aka shirya gudanarwa ranar Asabar an ɗage shi.
Taron dai an shirya gudanar da shi ne kan umarnin da ƙungiyar ECOWAS ta ba manyan hafsoshin tsaron na ɗaukar matakin ƙarfin soja a Jamhuriyar Nijar, cewar ahoton Channels tv.
An ɗage gudanar da taron har sai abin da hali ya yi duk kuwa da cewa ECOWAS ta umarci manyan hafsoshin nata da su kafa rundunar ko-ta-kwana domin kawo ƙarshen juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar da mayar da hamɓararren Shugaban ƙasar kan muƙaminsa.
Da Dumi-Dumi: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Sun Bayyana Ranar Dawowa Bakin Aiki
Kafin a ɗage gudanar da taron, an shirya yin taron ne a birnin Accra na ƙasar Ghana, kan yadda manyan hafsoshin tsaron za su yi wa ƙungiyar ECOWAS cikakken bayani kan hanyar da ta fi dacewa wajen yin amfani da rundunar ko-ta-kwanan da za a aike da ita zuwa Nijar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa aka ɗage taron?
Sai dai, daga baya an sanar da ɗage zaman sai abin da hali ya yi, saboda wasu dalilai da ba a bayyana su ba, rahoton Aminiya ya tabbatar.
Ɗage taron na zuwa ne bayan dubban al’ummar Nijar sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin ECOWAS na amfani da ƙarfin soja a ranar Juma'a.
A halin da ake ciki dai har yanzu ƙungiyar ECOWAS ba ta fitar da jadawali ko bayyana yanayin ƙarfin sojan da dakarun nata za su yi amfani da shi a Nijar ba, domin hamɓarar da juyin mulkin da sojojin suka yi ba.
Matsayar Sanatoci Kan Yaki Da Nijar
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatoci sun gayawa Shugaba Tinubu cewa ba batun yin yaƙi da Jamhuriyar Nijar.
Sanata Abdul Ningi wanda ya bayyana hakan, ya ce sanatocin ba su amince a yi amfani da sojojin Najeriya wajen yaƙi da Jamhuriyar Nijar ba.
Asali: Legit.ng