Majalisar ECOWAS Za Ta Gudanar Da Taron Gaggawa Ana Tsaka Da Rikicin Nijar

Majalisar ECOWAS Za Ta Gudanar Da Taron Gaggawa Ana Tsaka Da Rikicin Nijar

  • Majalisar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS ), ta sanar da cewar za ta gudanar da wani taro na musamman
  • Wannan taro na gaggawa zai kasance ne a kan juyin mulkin soja a Janhuriyar Nijar wanda Janar Abdourahamane Tchiani ya jagoranta
  • Ana sa ran taron na musamman zai tattauna kan matakai da hanyoyin magance rikicin da ke faruwa a Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Ana tsaka da fama da lamarin karbe mulki da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, majalisar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), za ta gudanar da wani taro na musamman.

An tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta.

Majalisar ECOWAS za ta yi taron gaggawa
Majalisar ECOWAS Za Ta Gudanar Da Taron Gaggawa Ana Tsaka Da Rikicin Nijar Hoto: ECOWAS Parliament
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa, za a gudanar da zaman ne ta yanar gizo a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, da karfe 10 na safe.

Kara karanta wannan

Kungiyar AU Ta Fadi Shirinta Na Taimakon ECOWAS Kan Afkawa Nijar, Bayanai Sun Fito

Sanarwar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta gudanar da wani taro na musamman domin tattauna batutuwan da suka shafi lamarin siyasar baya-bayan nan a Jamhuriyar Nijar.

"An shirya yin taron ne wanda zai gudana ta yanar gizo, a ranar Asabar, 12 ga watan Agustan 2023 da misalin karfe 10 na safe (agogon Najeriya).
“A cikin yanayin gagaruman sauye-sauyen da suka faru a fagen siyasa da tattalin arzikin duniya a karshen shekarun 1980, kasashe kungiyar ECOWAS da dama sun zage damtse wajen daukar kwararan matakai don samun zaman lafiya da tsaro ta hanyar bunkasa dimokradiyya da shugabanci nagari a farkon shekarun 1990.
"Saboda haka, matsayin ECOWAS akan Dimokradiyya da kyakkyawan shugabanci ya fara aiki a shekarar 2001, wanda ke nuna wani muhimmin mataki a ci gaban siyasar yankin. Gwamnatin soja da tsarin jam'iyya daya ya sa aka samu bullar dimokradiyyar jam'iyyu da dama"

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Jerin Kasashe 6 Na Afirka Ta Yamma Da ECOWAS Ta Afkawa A Nahiyar, Bayanai Sun Fito

Ana sa ran taron jam'iyyar zai samu gaba daya mambobin majalisar 115 wadanda za su tattauna kan hanyoyin da za a bi wajen hana keta dokokin kundin tsarin mulkin ECOWAS da wasu kasashe kamar Mali, Guinea, Burkina Faso da na bayan nan Jamhuriya Nijar ke yi.

Malamin addini ya gargadi ECOWAS kan daukar matakin soja a Nijar

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele ya aika gagarumin sako ga shugabannin Yammacin Afrika karkashin inuwar kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS).

Shahararren malamin ya bukaci shugabannin kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da su sake tunani kan ayyana matakin soja a kan gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng