Nijar: Malamin Addini Ya Bayyana Abun da Zai Faru Idan ECOWAS Da Tinubu Suka Ki Neman Sulhu
- Wani shahararen faston Najeriya ya yi martani a kan yunkurin ECOWAS karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- A cewar malamin addinin, amfani da karfi ba shine mafita ba a kan shugabannin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
- Sai dai kuma ya bayyana cewa idan shugabannin na Yammacin Afrika suka ki amfani da neman sulhu, za su biya bashi mai karfi, domin gwamnatin mulkin soji ba za ta girgiza ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele ya aika gagarumin sako ga shugabannin Yammacin Afrika karkashin inuwar kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS).
Nijar, Primate Ayodele ya bayyana abun da zai faru idan ECOWAS ta ki amfani da sulhu
Shahararren malamin ya bukaci shugabannin kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da su sake tunani kan ayyana matakin soja a kan gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar, Nigerian Tribune ta rahoto.
na zuwa ne bayan kungiyar ECOWAS ta ayyana daukar matakin soja cikin gaggawa kan gwamnatin mulkin soja a jiya a wani taro da ta gudanar a Abuja, Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku nemi taimakon Allah maimakon daukar matakin soja, Ayodele
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu, Primate Ayodele ya bayyana cewa yaki ba shi ne mafita ba, kuma idan zaman sulhu bai yi tasiri ba, a kyale Jamhuriyar Nijar, domin idan aka fara yakin za a kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, rahoton Daily Independent.
Sai dai ya bukaci shugabannin da su nemi taimakon Allah maimakon amfani da hankali.
Bazoum da dansa na cikin wani hali, ECOWAS
A gefe guda, mun kawo a baya cewa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi karin haske kan yanayin da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da dansa suke ciki.
Kwamishinan kungiyar ECOWAS kan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce Bazoum da dansa suna cikin mugun yanayi a tsare a hannun masu juyin mulki.
Musah ya bayyana hakan ne a yayin da ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng