Nijar: Sojoji 3 Da Suka Zama Ministoci Bayan Sun Taimaka An Kifar Da Gwamnati

Nijar: Sojoji 3 Da Suka Zama Ministoci Bayan Sun Taimaka An Kifar Da Gwamnati

Yamai, Jamhuriyar Nijar - Uku daga cikin Janar ɗin sojojin da suka taimaka wajen hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, an naɗa su ministoci a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sojojin suna daga cikin mutum 21 da aka ba muƙamin ministoci a gwamnatin mulkin soji ta Jamhuriyar Nijar.

Sojojin da aka ba ministoci a Nijar
An ba sojoji uku mukamin ministoci a Nijar Hoto: @stanislas_poyet, @FranklinNYAMSI, @GeneralTchiani
Asali: Twitter

Wani rahoton Al Jazeera na ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, ya bayyana sunayen su a matsayin Laftanar Janar Salifou Mody, Birgediya Janar Mohamed Toumba da Kanal Manjo Abdourahamane Amadou.

An ba su muƙamin ministoci na ma'aikatun tsaro, cikin gida da wasanni.

Legit.ng ta yi rubutu akan waɗannan sojojin guda uku dake cikin gwamnatin Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1) Laftanar Janar Salifou Mody

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Tsohon shugaban ma'aikata Laftanar Janar Mody wanda ake yi wa kallon zai zama mataimakin shugaban ƙasa, an ba shi muƙamin ministan tsaron ƙasa.

A ranar 1 ga watan Yunin 2023 aka naɗa Mody mai shekara 60 a duniya jakadan Nijar a haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE).

Ya riƙe muƙamin shugaban ma'aikata na hukumar sojojin Nijar daga shekarar 2020 zuwa 2023.

2) Birgediya Janar Mohamed Toumba

Birgediya Janar Toumba an ba shi muƙamin ministan cikin gida.

Toumba yana ɗaya daga cikin na gaba-gaba a cikin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar. Yana daga cikin sojojin da suka halarci gangamin nuna goyon baya da aka yi a babban birnin ƙasar Yamai a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta.

3) Kanal Manjo Abdourahamane Amadou

Kanal Amadou an bayyana sunansa a matsayin ministan wasanni na Jamhuriyar Nijar.

Amadou sojan sama ne wanda ya riƙe muƙamin kakakin sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula a Nijar, sannan suka ɗora Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Fargabar Yaƙi: Jerin Jihohin Najeriya 7 da Suka Haɗa Boda da Jamhuriyar Nijar

Shi ne yake karanto sanarwowin da sojojin su ke fitarwa a gidan talbijin tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin da ya gabata.

Tsohon Sarkin Kano Ya Isa Nijar

A wani labarin kuma, tsohon Sarkin Kano kuma Khalifan Darikar Tijjani na Najeriya, Sanusi II, ya ziyarci sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Muhammad Sanusi ya kai ziyarar ne domin tattaunawa da sojojin ta yadda za a samu maslaha kan rikicin shugabancin na Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng