ECOWAS Ta Umurci Sojojinta Su Ɗaura Ɗamarar Yaƙar Sojojin Nijar, Bayanai Sun Fito
- Kungiyar ECOWAS ta umurci dakarunta su daura damarar yaki da sojojin juyin mulki na Nijar
- Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin na kasashen Afirka ta Yamma ta cimma wannan matsayar ne a taro na musamman da ta yi ranar Alhamis a Abuja
- Wannan matakin na zuwa ne yayin da wa'adin kwana bakwai da ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su mayar da Bazoum ya cika
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugabannin kasashen da ke kungiyar ECOWAS sun bayar da umurnin dakarun sojojin kungiyar su daura damar kai yaki Jamhuriyar Nijar da sojoji suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.
Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Aliu Toure ne ya sanar da hakan yayin karonta sakon bayan taron sirri da suka gudanar a ranar Alhamis 10 ga watan Agusta a Abuja, Najeriya.
Juyin Mulkin Nijar: Jerin Kasashe 6 Na Afirka Ta Yamma Da ECOWAS Ta Afkawa A Nahiyar, Bayanai Sun Fito
ECOWAS ta umurci dakarunta su daura damar yaki da sojojin juyin mulkin Nijar
Shugabannin na ECOWAS sun bayar da wannan umurnin ne ga dakarunsu da nufin tilastawa sojojin da ke mulkin Nijar amincewa da kudirorinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A yanzu, babu tabbas ko wannan umurnin na nufin sojojin na ECOWAS za su far wa Nijar da yaki ne, ko kuma kawai su daura damara su kasance cikin shirin ko ta kwana ne.
Da farko dai, ECOWAS ta bai wa sojojin juyin mulkin wa'adin kwana bakwai su mayar da mulki ga Shugaba Bazoum ko kuma su fuskanci mataki na soji.
Amma, kungiyoyi da dama da mutane dai-dai ku masu fada a ji da sauran al'umma musamman a Najeriya sun nuna rashin amincewarsu da daukan matakin sojin kan Nijar, suna masu bayar da shawarar a cigaba da tattaunawa.
Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Jawabi a Taron ECOWAS
Tunda farko, Legit.ng Hausa ta rahoto Shugaba Bola Tinubu ya ayyana cewa Hukumar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, za ta fi mayar da hankali kan tattaunawa domin kawo karshen rikicin siyasa da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne yayin bude taro na musamman na shugabannin kasashen na Afirka ta Yamma a ranar Alhamis 10 ga watan Agusta.
Juyin Mulkin Nijar: Shugabannin ECOWAS sun yi taron gaggawa a Abuja
Shugabannin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, sun yi taron gaggawa a Abuja kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, a ranar Alhamis 10 ga watan Agusta a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Shugabannin na ECOWAS daga kasashe 15 za su dauki muhimmin mataki kan wa'adin sati biyun da suka bai wa sojojin Nijar.
Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng