An Halaka Dan Takarar Shugaban Kasar Ecuador Har Lahira a Wajen Yakin Neman Zabe
- Ɗan takarar shugaban ƙasar Ecuador, Fernando Villavicencio ya gamu da ajalinsa a wajen wani gangamin yaƙin neman zaɓe
- An halaka ɗan takarar ne bayan an buɗe masa wuta lokacin da yake ƙoƙarin shiga mota bayan kammala yaƙin neman zaɓen
- Hukumomi sun yi Allah wadai da harin inda suka sha alwashin zaƙulo waɗanda suka aikata aikin ta'addancin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ecuador - An bindige ɗan takarar shugaban ƙasar Ecuador, Fernando Villavicencio, har lahira a wajen wani gangamin yaƙin neman zaɓe a birnin Quito.
Hukumomi sun bayyana cewa ɗan siyasar an halaka shi ne a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, rahoton RT ya tabbatar.
An halaka ɗan siyasar ne mai shekara 59 a duniya lokacin da yake barin wajen wani taron yaƙin neman zaɓe a babban birnin ƙasar Ecuador, inda hadiminsa Carlos Figueroa ya tabbatar da cewa an yi masa harbi uku ne a kai.
Martanin shugaban ƙasar Ecuador
Shugaban ƙasa Guillermo Lasso ya yi magana kan harbin a cikin wata sanarwa da aka sanya a soshiyal midiya, inda ya bayyana cewa ya ji takaici da kaɗuwa matuƙa kan kisan da aka yi wa Fernando Villavicencio.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ƙara da cewa aikin ta'addancin ya yi muni sosai sannan ya bayar da tabbacin cewa za a zaƙulo waɗanda suka aikata kisan.
Wani faifan bidiyo da ya yaɗu a yanar gizo ya nuna lokacin da aka gudanar da harbin, inda aka ji ƙarar harbe-harben bindiga lokacin da jami'an tsaro su ke raka Villavicencio zuwa cikin motarsa bayan wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Quito.
Figueroa ya bayyana cewa lokacin da ya duba ɗan takarar bayan harin ya tabbatar da baya numfashi, inda aka tabbatar da mutuwarsa a wani asibiti dake kusa da wajen, cewar rahoton Sahara Reporters.
Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito
Shin an cafke masu kai harin?
A cewar Antoni Janar na ƙasar Ecuador, an cafke wani mutum ɗaya da ake zargi da hannu wajen harbe-harben amma ya mutu daga baya a sakamakon raunikan da ya samu a musayar wutar da ya yi da jami'an tsaro.
Mutum tara ne suka samu raunika a yayin harin, ciki har da jami'an tsaro guda biyu da wani ɗan takara guda ɗaya.
Ƴan sanda sun bayyana harin a matsayin aikin ta'addanci sannan suka sha alwashin gudanar da bincike.
Tsohon Shugaban 'Yan Tawaye a Nijar Ya Kaddamar Da Sabuwar Kungiya
A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƴan tawaye a Jamhuriyar Nijar, ya ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar za ta fafata da sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar.
Rhissa Ag Boula, ya kaddamar da wata kungiya domin adawa da masu juyin mulki, wadanda suka hambarar da Shugaban kasa Mohamed Bazoum daga karagar mulki.
Asali: Legit.ng