Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

  • Asari Dokubo, tsohon shugaban kungiyar tsagerun Niger Delta, ya yi martani kan halin da ake ciki dangane da juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
  • Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta ki sauka daga karagar mulki, ta kuma kafa gwamnatinta domin fara gudanar da harkokin shugabanci
  • Dokubo ya bugi kirjin cewa yana da yawan mutane da kayayyakin da ake bukata domin cin galaba a kan shugabannin juyin mulkin Nijar idan FG da ECOWAS suka ba shi dama

Tsohon shugaban kungiyar tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo, ya bugi kirjin cewa zai yi kasa-kasa da masu juyin mulki a Nijar da dakarunsu idan har gwamnatin tarayya da kungiyar ECOWAS suka daura masa alhakin yin haka.

Dokubo wanda ya kasance mutum mara tsoro ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya yadu kuma Legit.ng ta gani a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Dokubo ya nemi a ba shi dama ya yi maganin gwamnatin sojan Nijar
Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayinda Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar Hoto: @abati1990
Asali: UGC

Dokubo ya bayyana cewa yana da yawan mutane da kayan da zai iya fafatawa da sojojin Nijar a fadan jiki da na bindiga idan ana bukata.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

’Idan gwamnati ta umurce ni damutane na mu je Jamhuriyar Nijar, za mu je. Za mu ci galaba a kansu, kuma za mu dawo da nasara. Ba fariya ba ne.
"Idan Jamhuriyar Nijar ta so; su je su kawo koma wanene; suma mutane ne kamar mu. Za mu je chan, mu ci galaba a kansu sannan mu dawo da tsarin damokradiyya."

Jama'a sun yi martani

A daya bangaren, Dokubo ya sha caccaka a soshiyal midiya kan ikirarinsa na cewar zai lallasa Nijar da mayakansa.

@Oxzejenn ya ce:

"Lalatacciyar gangan. Yakin Creek da yakin Sahara ba iri daya ba ne. Idan ka iya iyo a ruwa ba yana nufin za ka iya tafiya a kan yashi mai zafi ba."

Kara karanta wannan

Bazoum: 'Gayar Shinkafa' Na Ke Ci Yanzu, Hambararen Shugaban Nijar Ya Koka

@ikechukwumogaha ya ce:

"Ku dubi wannan wanda shi ba sojan soja ba kuma bai da kwarewar sosjoji, yana so ya fuskanci mulkin soja da kawayenta na Rasha .. "

@luvinngs ya ce:

"Kana tunanin dodon Ogoni ne da zai hana ka mutuwa a Nijar...Nijar za su kashe ka kamar sauro....Ya ce hukuma, kan me ma ko a matsayin me....dan wasan barkwanci Asari."

Sojin Jamhuriyar Nijar Sun Kafa Sabuwar Gwamnati Mai Minitoci 21

A wani labarin kuma, Shugaban sojin Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya kafa sabuwar gwamnati mai dauke da ministoci 21 a kasar.

Tchiani ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta kafar talabijin a ranar Laraba 9 ga watan Agusta da dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng