Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sojoji Zuwa Jamhuriyar Nijar? Gaskiya Ta Fito
- Hedikwatar hukumar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta musanta rahoton cewa Shugaba Bola Tinubu ya shirya yin amfani da ƙarfin soja akan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
- Hukumar tsaron ta Najeriya ta bayyana cewa ba ta samu wani umarni ba kan yin amfani da ƙarfin soja daga hukumomin da suka dace
- Birgediya Janar Tukur Gusau, muƙaddashin darektan watsa labarai, ya ce sojojin Najeriga ba za su afka cikin ƙasashen ECOWAS ba sai da cikakken umarni
FCT, Abuja - Hedikwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta yi magana kan jita-jitar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin amfani da ƙarfin soja a Jamhuriyar Nijar.
Hukumar tsaron ta Najeriya ta bayyana cewa ba ta samu wani umarni ba daga hukumomin da suka dace, domin yin amfani da ƙarfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, cewar rahoton The Sun.
Hakazalika, hukumar tsaron ta bayyana cewa ba za ta iya yin aikin soji a ɗaya daga cikin ƙasashen ECOWAS ba har sai shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun sahale mata yin hakan.
DHQ ta yi magana kan batun Shugaba Tinubu ya aike da sojoji zuwa Nijar
Birgediya Janar Tukur Gusau, muƙaddashin darektan watsa labarai na hukumar, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a birnin tarayya Abuja, ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gusau ya bayyana cewa rahoton ƙarya ce tsagwaronta, inda ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da shi, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Amfani da ƙarfin soja shi ne zaɓin ƙarshe idan har sauran hanyoyin da za a bi sun ƙare domin dawo da gwamnatin Jamhuriyar Nijar kan turbar amfani da kundin tsarin mulki."
Ya kuma ƙara da cewa hafsoshin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun tattauna a birnin tarayya Abuja, domin miƙa shirye-shiryen da su ke da su ga shugabannin ECOWAS.
Najeriya Ta Katse Wutar Lantarkin Da Take Ba Nijar
A wani labarin kuma, an shiga duhu a wasu birane na Jamhuriyar Nijar bayan Najeriya ta katse wutar lantarkin da take ba ƙasar.
Katse wutar lantarkin na zuwa ne yayin da ƙungiyar ECOWAS ke ƙara matsin lamba ga sojoji su bar madafun iko a Jamhuriyar Nijar.
Asali: Legit.ng