Farai Ministan Canada Ya Saki Matarsa Bayan Shekaru 18 Da Aure

Farai Ministan Canada Ya Saki Matarsa Bayan Shekaru 18 Da Aure

Canada - Justin Trudeau, Farai ministan Canada da matarsa, Sophie sun rattaba hannu kan takardan raba aurensu bayan kusan shekaru 18 suna aure.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Trudeau ya sanar da hakan ne a shafinsa na Instagram a yammacin ranar Laraba.

Auren Firai Ministan Canada Da Matarsa Ya Mutu Bayan Shekaru 18
Farai Ministan Canada Ya Rabu Da Matarsa Bayan Shekaru 18. Hoto: Jacob King/PA Images via Getty
Asali: Getty Images

Ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Barka dai, Sophie da ni muna son mu sanar da cewa bayan tattaunawa mai wahala da ma'ana, mun yanke shawarar mu rabu.
"Kamar yadda aka saba, za mu cigaba da kusanci a iyali tare da kauna da girmama juna da abin da muka gina kuma za mu cigaba da ginawa. Saboda walwalar yaranmu, muna rokon ku mutunta sirrin mu da na yayanmu. Mun gode."

Ofishin Trudeau ita ma ta tabbatar da rabuwar firaiministan da matarsa

Kara karanta wannan

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

Hakazalika, ofishinsa ita ma ta tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce:

"Sun yi aiki don tabbatar da cewa an bi dukkan dokokin kotu dangane da niyyarsu ta rabuwa, kuma za su cigaba da yin hakan nan gaba.
"Za su cigaba da kasancewa iyali kuma Sophie da Faraiministan za su mayar da hankali don kula da yaransu a yanayi na kauna, tsaro da hadin kai. Iyalan za su tafi hutu, daga mako mai zuwa."

Trudeau, dan shekara 51, da Sophie, yar shekara 48, sun yi aure a Mayun 2005. Sun haifi yara uku tare.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164