Shugaba Tinubu Ya Bi Sahun Buhari, Zai Samu Mukamin Shugabancin ECOWAS

Shugaba Tinubu Ya Bi Sahun Buhari, Zai Samu Mukamin Shugabancin ECOWAS

  • Ƙungiƴar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) na shirin yin sabon shugaban da zai jagoranceta
  • Shugaba Bola Tinubu zai karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar a hannun shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo
  • Ko a shekarun baya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taɓa riƙe kujerar hugabancin ƙungiyar ta ECOWAS

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugaban ƙasa Bola Tinubu na shirin zama shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS), cewar rahoton The Cable.

Shugaba Tinubu, wanda ya bar Abuja a ranar Asabar domin halartar taron shugabannin ƙasashen, ana sa ran zai karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar daga hannun Umaro Sissoco Embaló na ƙasar Guinea-Bissau, majiyoyin diflomasiyya suka gagawa jaridar.

Shugaba Tinubu zai zama shugaban ECOWAS
Majiyoyi sun ce Shugaba Tinubu zai zama shugaban ECOWAS Hoto: @DOlusegen
Asali: Facebook

Taron karo 63 na shugabannin ƙasashen za a gudanar da shi ne a birnin Bissau, babban birnin ƙasar Guinea-Bissau.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Tinubu, Shugaban NPC Ya Yi Magana Kan Sabuwar Ranar da Za'a Yi Ƙidaya a Najeriya

Tsohon shugaban ƙasa Muhammdu Buhari ya taɓa riƙe muƙamin a shekarar 2018.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu, wanda ya gaji Buhari a shugabancin Najeriya a watan Mayun 2023, wannan ne karonsa na farko da yake fita zuwa taro a nahiyar Afirika.

Ya halarci taro kan harkar tattalinx arziƙi a ƙasar Faransa a ƙarƙashin jagorancin Emmanuel Macron, shugaban ƙasar Faransa a watan Yuni.

Maƙasudin taron na ECOWAS

Taron na shugabannin ƙasashen da ke a ƙungiyar ECOWAS zai tattauna kan batutuwan da suka shafin yankin, da suka haɗa da matsalar tsaron da wasu daga cikin ƙasashen ke fama da ita da batun tattalin arziƙi.

Taron zai duba batun kaɗɗamar da kasuwanci ba tare da wani shamaki ba a nahiyar Afirika da rahoto kan halin miƙa mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso da Guinea.

A shekara 1975 aka kafa ƙungiyar ECOWAS inda yanzu haka ta ke da mambobi 15 da yawan al'umma 387m.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Wakilan Bankin Amurka, Bayanai Sun Fito

Ƙasashen sun haɗa da Benin, Burkina Faso, Cape Verde, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Ivory Coast, Liberia, Mali, Nijar, Najeriya, Senegal, Sierra Leone da Togo.

Shugaba Tinubu Zai Taka Kasar Afirika

A baya an samu rahoton cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai shilla ƙasar waje ta farko a nahiyar Afirika ɗomin halartar taro.

Shugaban ƙasan zai halarci taron ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (EOWAS) a ƙasar Guinea-Bissau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng