Fafaroma Francis Ya Yi Allah Wadai Da Kona Kur’ani Da Wasu Mutane Suka Yi a Sweden
- Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da kona Kur'ani mai girma da wasu mutane biyu suka yi a kasar Sweden
- Fafaroma ya ce dole ne a mutunta duk wani littafi da wasu suka dauka a matsayin mai tsarki kuma suke mutunta shi
- Kasashen Musulmi da dama ciki har da Saudiyya, sun nuna bacin ransu ga Gwamnatin Sweden bisa faruwar lamarin
Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da kona Kur’ani mai girma da ya faru cikin 'yan kwanakin nan, a birnin Stockholm, da wasu mutane biyu suka yi.
Rahotanni sun bayyana cewa Fafaroma Francis ya fusata ainun gami da nuna kyamatarsa a fili game da kona Kur'anin da aka yi, kamar yadda Premium Times ta wallafa.
A kalaman Fafaroma:
"Duk wani littafi da aka dauka mai tsarki dole ne a mutunta shi domin girmama wadanda suka gaskata da shi, kuma bai kamata a yi amfani da 'yancin fadin albarkacin baki a matsayin hujjar raina wasu ba."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Fafaroma ya kara da cewa hakan abu ne da ya kamata a yi watsi gami da Allah wadai da shi.
Wasu mutane biyu da suka halarci zanga-zanga a babban birnin kasar Sweden, sun cinnawa Al-Kur'ani mai tsarki wuta a a ranar Laraba, wacce ta yi daidai da ranar Idin babbar sallah.
Saudi Arabiya da wasu kasashen Musulmi sun yi Allah wadai da kona Kura'ani a Sweden
Kasashen musulmi da dama sun yi Allah wadai da lamarin tare da kakkausar suka ga jami'an diflomasiyyar Sweden.
Kasashen sun bayyana cewa matakin ya janyo kiyayya, kuma bai kamata a kalle shi a matsayin 'yancin fadin albarkacin baki ba.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudi Arabiya a ranar Lahadin da ta gabata ta gayyaci jakadan kasar Sweden a Riyadh don bayyana masa kin amincewar da masarautar ta yi kan abin kunyan da wani mai tsatsauran ra'ayi ya yi.
Kone Al-Qur'ani a Sweden: Kungiyar Musulmai Ta Fadi Matakan Da Za Ta Dauka Don Kare Martabar Alkur'ani A Fadin Duniya
Haka nan ta yi kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki kan duk wasu ayyukan da suka saba wa kokarin kasa da kasa na neman yada dabi'un hakuri, daidaito da kuma watsi da tsattsauran ra'ayi, kamar yadda Aljazeera ta wallafa.
Kiran na Saudiya ya ci gaba da cewa:
"Bai kamata Gwamnatin Sweden ta lalata dangantakar da ke tsakanin mutane da kasarta ba."
A nata bangaren, Gwamnatin Sweden ta ce abinda mutanen suka yi daidai ne a karkashin dokokin 'yancin fadin albarkacin baki na kasar, amma sai dai bai dace ba.
Kungiyar CAN ta soki Nasiru El-Rufai bisa kalaman da ya yi kan tikitin Muslim-Muslim
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa, kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Kaduna ta soki tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai bisa kalamansa kan tikitin Muslim-Muslim.
John Joseph Hayab, shugaban kungiyar reshen jihar Kaduna ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng