Barayi Sun Tafkawa Fafaroma Benedict Gagarumar Sata, Sun Sace Abu Mai Muhimmanci Ga Kiristoci
- 'Yan sanda a ƙasar Jamus, sun bayyana cewa wasu da ba a san ko su waye ba, sun fasa coci gami da ɗauke kuros ɗin tsohon Fafaroma, Benedict XVI
- Yan sandan sun kuma ce, mutanen sun yi awon gaba da wasu kuɗaɗe masu tarin yawa a yayin da suke satar
- Tsohon shugaban mabiya ɗariƙar Katolika ta duniya, Fafaroma Benedict XVI ya sadaukar da kuros ɗin ne ga wata coci da ke a mahaifarsa Bavaria
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
'Yan sandan ƙasar Jamus, a jiya Talata, sun bayyana cewa an sace kuros ɗin da tsohon Fafaroma, Benedict XVI, ya saba sanyawa a ƙirjinsa daga wata coci da ke kudancin ƙasar.
An ce Fafaroma Benedict ya sadaukar da kuros ɗin da aka sace ga wata coci da ke mahaifarsa, wato Bavaria da ke ƙasar Jamus, kamar yadda ABC News ta wallafa.
Barayin sun haɗa da satar kuɗi baya ga kuros ɗin
Yan sandan sun bayyana cewa barayin da ba a san ko su waye ba, sun tafka mummunar satar ne a tsakanin ƙarfe 11:45 na safe zuwa 05:00 na yammacin ranar Litinin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sun kuma ƙara da cewa, baya ga kuros ɗin da ɓarayin suka sace, sun kuma ɗebi kuɗaɗe masu tarin yawa kamar yadda ABC.com ta ruwaito.
Yan sandan sun kuma ce kuros ɗin da aka ɗauke, irin wanda ake ratayawa a wuya ne mai sauka akan ƙirji.
'Yan sanda na gudanar da bincike kan satar kuros ɗin
Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce jami'an tsaro sun ƙaddamar da bincike kan satar, inda suke kiran mutane suna amsa tambayoyi dangane shige da ficen da mutane suka yi a kusa da cocin.
Bayanin 'yan sandan ya ƙara da cewa, kuros ɗin da aka sace wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ga mabiya ɗarikar katolika, inda suka nemi waɗanda suka ɗauka su dawo da shi.
A shekarar 2022 ne dai aka dawo da kuros ɗin zuwa cocin da aka sace shi, bayan murabus daga shugabancin da Fafaroma Benedict XVI ɗin ya yi, wanda kuma ya rasu a ƙarshen shekarar.
Fafaroma Benedict ne mutum na farko da ya taɓa ajiye muƙaminsa na shugabancin mabiya ɗarikar ta katolika a cikin sama da shekaru 60 da suka gabata.
Limamin cocin birnin Munich, Christoph Kappes, ya ce irin kuros ɗin da aka sace ba shi da yawa a duniya.
'Yan sanda sun cafke wata mata da ta damfari mutane kuɗi a Neja
Legit.ng a wani rahoto, ta kawo muku labarin wata mata da 'yan sanda suka yi ram da ita sakamakon damfarar mutane da ta yi a Neja.
An zargi matar, mai suna Damilola da damfarar mutane maƙudan kuɗaɗe har miliyan 150.
Asali: Legit.ng