Rasha: Shugabannin Kasashen Afrika 7 Sun Tafi Turai Don Shiga Tsakani Kan Rikicin Rasha da Ukraine
- Shugabannin ƙasashen Afrika 7 ne suka tafi zuwa Turai don shiga tsakani a rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin ƙasashen Ukraine da Rasha
- Shugabannin za su gana da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky daban-daban
- Shugabannin sun ɗauri aniyar nemo hanyar warware rikicin da ke faruwa cikin lumana, tare da tattauna yiwuwar ƙara yawan hatsi da taki zuwa ƙasashen Afrika
Tarayyar Turai - Shugabannin ƙasashen Afrika bakwai ne dai aka tabbatar da tafiyarsu zuwa nahiyar Turai domin taimakawa wajen sasanta rikicin da ke wakana tsakanin Rasha da Ukraine.
A ranar Juma'ar nan ake sa ran za su gana daban-daban da shugaban Rasha Vladimir Putin, da kuma shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, kamar yadda kafar TRT ta wallafa.
Shugabannin ƙasashen Afrika bakwai da suka tafi Rasha da Ukraine sasanci
Shugabannin dai na da burin ganin an warware tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane, da kuma janyo hasarar dukiya mai tarin yawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, na cikin tawagar, tare da shugabannin ƙasashen Zambia, Comoros, Congo Brazzaville, Masar, Senegal, da Uganda.
Sai dai shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni, bai samu shiga cikin tawagar ba saboda ci gaba da murmurewa da yake daga cutar COVID-19, inda ya tura da wakilci.
Shugabannin ƙasashen na Afrika za su tattauna ba wai iya rikicin kaɗai ba, har da makomar fitar da hatsi mai inganci ta yankin tekun Black Sea na Ukraine zuwa nahiyar ta Afrika.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa shugabannin na Afrika fatan alkhairi
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana fatan samun sakamako mai kyau daga tattaunawar da Shugaba Putin zai yi da shugabannin na Afrika.
Ziyarar ta zo ne jim kadan bayan da Ukraine ta ƙaddamar da wani babban mataki na kai hare-hare a makon jiya da take fatan zai taimaka wajen ƙwato yankunan da sojojin Rasha suka mamaye a kudanci da gabashin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai, Reuters ya ruwaito.
Yadda ake dakon muƙaman Ministocin Tinubu a jihohin Najeriya
A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da naɗin masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban na gudanar mulki.
Hakan ya sanya wasu jiga-jigai a jihohi da suka haɗa da tsoffin gwamnoni da tsoffin ministoci fara dakon Tinubu ya nemi a miƙa sunayen waɗanda yake so ya bai wa muƙaman ministocinsa.
Asali: Legit.ng