Kasashen Afirka 10 Da Suke Biyan Mafi Karancin Albashin Ma'aikata Fiye Da Na Najeriya
- Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke biyan mafi ƙasa na karancin albashin ma'aikata a nahiyar
- Mafi ƙarancin albashin Najeriya a yanzu N30,000 ne, wanda ya ke daidai da kusan dalar Amurka 64.7 idan aka canza shi zuwa farashin CBN
- A kwanakin baya ne Najeriya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya sa ma’aikata a Najeriya suka buƙaci a kara musu mafi karancin albashin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Biyo bayan cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi, ma'aikata a Najeriya sun fara tado da batun ƙarin mafi ƙarancin albashin da ake ba su a yanzu.
Manazarta na ganin cewa Najeriya ce kusan ta ƙasa a biyan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a nahiyar Afirka, duk kuwa da cewa ita ce ƙasa mafi karfin tattalin arziƙi a nahiyar.
N30,000 ba ta isar ma'aikatan wajen kwaranniyoyinsu
A Najeriya, an ƙayyade mafi ƙarancin albashin a dalar Amurka 64.7, kimanin N30,000 a farashin canjin dala na N463 da babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙayyade.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babbar fargabar ma’aikatan dai ita ce, yadda mafi ƙarancin albashin da gwamnatin Najeriya ke biya a halin yanzu da kyar yake iya biya musu buƙatunsu.
Ma'aikatan sun ƙara shiga fargaba, biyo bayan cire tallafin man fetur da ya yi sanadin tashin farashin man da kuma tashin gwauron zabi na kayayyakin masarufi, harkokin sufuri da sauransu.
Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci gwamnati ta karawa ma'aikata albashi
Akan haka ne ma ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya suka yi barazanar shiga yajin aiki a duk faɗin ƙasar sakamakon ƙarin farashin man fetur ɗin.
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun buƙaci gwamnati ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata, wanda a halin yanzu yake a N30,000.
Jerin Jami'o'in Da Suka Kara Kudin Makaranta Tun Bayan Da Aka Sanya Hannu Kan Dokar Ba Dalibai Bashi
A cewar Nairametrics, ƙungiyar kwadago ta ƙasa (TUC), ta bayyana buƙatunta ga gwamnati bayan janye yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar sakamakon cire tallafin man fetur.
Ma'aikata sun bayyana bukatarsu
A wata sanarwa dake ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar, Festus Osifo, da babban sakataren kungiyar, Mista Nuhu Toro, a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023, TUC ta gabatar da jerin buƙatunta ga Gwamnatin Tarayya.
Buƙatun sun haɗa da a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N200,000 daga N30,000 da ake biya a yanzu kafin karshen watan Yunin 2023.
Haka nan kuma sun buƙaci gwamnati ta ɗage karɓar haraji daga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke samun ƙasa da N200,000 ko $500.
Albashin ma'aikata a kasashen waje
Rahotanni sun bayyana cewa ƙasashe irin su Libya da ke fama da rikici, Seychelles, da wasu sauran ƙananun ƙasashen Afirka masu ƙaramin ƙarfi na biyan mafi karancin albashi ninki huɗu fiye da na Najeriya.
'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Farmaki a Arewacin Najeriya, Sun Salwantar Da Rayukan Bayin Allah Da Dama
A koda yaushe, gwamnatin Najeriyar na bayar da uzurin cewa tana fama da ƙarancin kuɗaɗen shiga, shi yasa take gaza bayar da albashi mai ɗan gwaɓi ga ma'aikatan ƙasar.
Ga jerin sunayen ƙasashe 10 da suka fi biyan mafi ƙarancin albashin a nahiyar Afirka:
- Seychelles: N200,000
- Libya: N149,000
- Maroko: N130,000
- Gabon: N118,000
- Afirka ta Kudu: N112,000
- Mauritius: N111,120
- Equatorial Guinea: N92,000
- Kongo: N71,000
- Algeriya: N70,000
- Kenya: N65,000
Kotu ta hana ƙungiyoyin ƙwadago shiga yajin aiki
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, kun ji cewa kotu ta dakatar da ƙungiyoyin kwaɗago shiga yajin aikin da suka yi shirin farawa ranar Laraba mai zuwa.
Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun yi barazanar tsunduma yajin aiki biyo bayan cire tallafin man fetur da ya sabbaba tashin gwauron zabin abubuwan amfani na yau da kullum.
Asali: Legit.ng