Tashin Hankalin Da Mu Ka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru

Tashin Hankalin Da Mu Ka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru

  • Bello Halliru, ɗaya daga cikin 'yan Najeriya da ke karatu a Sudan ya bayyana irin masifar da suka shiga a can
  • Ya bayyana cewa sun fuskanci tashin hankali mara misaltuwa ta dalilin tarzomar da ke faruwa a Sudan
  • Ya ce ba ya ma fatan Najeriya ta fuskanci irin ƙalubalen da Sudan ke fuskanta

Abuja - Aƙalla 'yan Najeriya 374 ne waɗanda aka samu damar kwasowa daga Sudan su ka sauka a babban filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da yammacin ranar laraba.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka samu damar kwasowar mai suna Halliru Bello wanda ɗalibin karatun likitanci ne a can Sudan ya shaida ma Daily Trust cewa baya fatan Najeriya ta fuskanci irin wannan rikici, domin kuwa zai iya daƙile 'yan ƙasa da ruguje al'amura baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

'Yan Najeriya da aka kwaso daga Sudan
'Yan Najeriya da aka kwaso daga Sudan. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rikicin ya shafi harkar karatu na

Ya ƙara da cewar wannan rikicin da ke faruwa a ƙasar ta Sudan ya shafi karatun shi matuƙa a matsayin shi na ɗalibin likitanci, domin kuwa ya janyo dole karatun da ya ke yi yanzu haka ya dakata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an soma rikicin da ƙarfe 11 na wata safiya, inda ya ce a wannan lokacin ne su ka fara jin ƙarar harbe-harbe. Bayan kwana uku da yin wannan kuma sai su ka fara ganin jiragen yaƙi na shawagi gami da harbo makamai masu linzami.

Bello ya ƙara da cewar daga nan kuma sai saƙo ya iso gare su cewar kada wanda ya fita waje don yi wani abu ko kuma domin zuwa kasuwa domin yin siyayya sabili da cewa ƙasa babu lafiya.

Ya ce tashin hankalin da su ka fuskanta ba ɗan kaɗan bane, sai wanda ya ke can ne kaɗai a lokacin da abin ya ke faruwa zai iya gane irin tashin hankalin. Bello ya ce bazai taɓa ma wani ya fatan ya fuskanci irin wannan tashin hankali ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Kasar Masar Ta Umarci Ɗaliban Najeriya Sama da 500 Su Koma Sudan Kan Halayyar Mutum 2

Ba na ma Najeriya fatan faɗawa cikin matsala ta tarzoma

Ya ce ya na fatan Najeriya ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ba ta fuskanci tarzoma ba. Harkokin ilimi sukan samu naƙasu, ta yadda ko abincin da mutum zai ci ma sai ya nemi ya gagare shi. Idan kuma mutum ya yi ƙoƙarin fita wajen to lallai yakan iya rasa ran shi a yayin musayar wuta.

Najeriya ta fi kowace ƙasa arhar wutar lantarki

A wani labarin na daban kuma, ministan wutar lantarki na ƙasa, Aliyu Abubakar, ya koka kan ƙin biyan kuɗin wuta da mutane da sauran manyan ma'aikatun gwamnati ke yi.

Ya ce duk da sauƙin da wutar Najeriya ta ke da ita, wacce itace mafi arha a duk duniya, amma a hakan da yawa daga cikin manyan ma'aikatun gwamnati basa biyan kuɗaɗen su a kan kari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng